Ina Ƙaunar Tsohon Sarki Faisal Na Saudiyya– Daga Aliyu Ibrahim S/Mainagge

4

Ƙasar Saudiyya tana fuskantar canje-canje a ɓangarorin siyasa, tattalin arziƙi da zamantakewa da uwa uba harkokin addini tun bayan naɗa Yarima Muhammad bn Salman, wanda aka fi sani da MBS, a matsayin Yarima Mai Jiran Gado. Waɗannan canje-canje sun haɗa har da sake fasalin harkokin addini a ƙasar da ake gani a matsayin alƙiblar Musulmi wajen gudanar da harkokin addinin Musulunci.
Yarima MBS, wanda yake a matsayin Mataimakin Firayiministan Ƙasar Saudiyya, kuma Shugaban Majalisar Tattalin Arziƙi da ci Gaban Ƙasa, kuma Shugaban Majalisar Harkokin Siyasa da Tsaro kuma Ministan Tsaron Ƙasar, shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya taɓa riƙe irin waɗannan muƙama a duniya.

Ana ganin Yarima MBS a matsayin mutumin da ya fi kowa ƙarfi a ƙasar tun bayan da aka ture Muhammad bn Nayef daga matsayin Yarima Mai Jiran Gado a watan Yunin 2017, kuma ana ganin hakan a matsayin share masa hanya ne na ɗare wa a matsayin Sarkin Saudiyya bayan mahaifinsa Sarki Salman bn Abdul’aziz.

Daga cikin canje-canjen da Yarima MBS ya kawo sun haɗa da rage ƙarfin dakarun Hisba, rage haramcin tuƙa mota ga mata, amincewa da mata su shiga kallon wasanni da raye-raye, ƙara fito da mata a harkokin ayyukan gwamnati, da kuma ƙara adadin masu shigowa ƙasar domin yawon buɗe ido da shaƙatawa, uwa uba da takura wa da hana malamai masu ƙoƙarin faɗin gaskiya sakewa a ƙasar. Wannan ya haɗa da hukuncin ɗauri ga duk malamin da ya soki alamuran tafiyar da gwamnati.

Duk da kuwa a ɓangare ɗaya, Yarima MBS na sukar Amurka a kan batun kafa ƙasar Yahudawa da kuma nuna goyan bayansa ga Musulmin Falasɗinu da kuma batun ƙasar Shia ta Iran.

Wannan mataki na waɗancan canje-canjen zamanin masana na ganinsa a matsayin wani alamari na cika muradun Turawa da suka daɗe suna aiki wajen ganin ƙasar ta Saudiyya ta amince da canje-canjen zamani da zai mayar da ƙasar a matsayin wadda ba ruwanta ko take da sassauci a harkokin addini.

Wannan ce ta sanya a kodayaushe na ga ko karanta wani abu dake da alaƙa da Saudiyya sai na tuna karin maganar Hausar dake cewa: “Kowat tuna bara bai ji daɗin bana ba. Domin hakan na tuna mini da Sarki Faisal ɗan Abdul’aziz (Allah ya yi masa rahama) da dagewarsa wajen ganin ba a yi sakaci da duk wani alamari da ya shafi addini da zamantakewar alummar Musulmi ba, kamar yadda wani masani yake cewa, game da ƙasar ta Saudiyya: A ƙasar Saudiyya, Musulunci ba kaɗai yana a matsayin addini a ƙasar ba, a’a, shi ne ma tsarin rayuwar gaba ɗaya, alummar ƙasar Saudiya, wannan ce ta sanya malamai ke da babban matsayi wajen tafiyar da gwamnati. (Duba Religion And The State. Na Natelie Goldstein, Brown Foster; Walton (2010).

A shekarar 1906 ne aka haifi Sarki Faisal ɗan Abdul’aziz a Riyadh, babban birnin ƙasar Saudiyya. Shi ne ɗa na uku a wajen babansa, Abdul’aziz.
Tun da yarintarsa mahaifinsa ya sanya shi ayyuka masu yawa na shaanin mulkin ƙasa. A shekarar 1925, ya zama Kwamandan Sojojin Saudiyya, ya zama Gwamnan Hijaz da ta haɗa Makka da Madina a shekarar 1926. (Duba King Faisal Al-Saud In The Arena Of World Politics: A Glimpse From Washington 1950-1971. British Journal of Middle Eastern Studies 31 (1). Helmut, Mejcher).

Shekaru shida bayan haka, a shekarar 1932, ya zama Ministan Harkokin Waje, muƙamin da ya riƙe har ya zama Sarkin Ƙasar. (Official Website Of Saudi Ministry of Foreign Affairs 1 ga 27 March, 2007).

A matsayinsa na Sarkin Saudiyya, Faisal ɗan Abdul’aziz ya yi ƙoƙari matuƙa da gaske wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, musamman bayan Yaƙin Duniya na Biyu, ya ƙara yawan kuɗin da ake samu na man fetur daga dala miliyan ($10.4 million) a shekarar 1946 zuwa dala miliyan $56.7 a shekarar 1950.

Haka kuma ya yi ƙoƙari ƙwarai a harkar tafiyar da mulkin alummarsa, a ɓangaren zamantakewa da hulɗa da ƙasashen waje duka tsohon Sarkin ya ba da muhimmiyar kulawa. (Oil And The State In Saudi Arabia. Steffen Hertog, (etal), Ithaca: Cornell up, 2010 Print).

Daga mafi girman aikin da ya yi wa Musulunci shi ne taimakawarsa wajen kafa Jamiar Musulunci ta Madina, Birnin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) a shekarar 1961, jamiar da ta zama shahararriya a ɓangaren bada ilimin addinin Musulunci, wadda ɗaruruwan ɗalibai daga Najeriya suka sami damar halartarta da samun ilmi mai ɗimbin yawa a cikinta. Haka kuma ya gayyato malamai masu yawa daga ƙasashen Musulmi musamman Misra domin koyarwa a Jamiar Musuluncin domin samun wayewa da ilmi daga ɓangarorin malamai na duniya. Wannan ce ta sanya tsohon Sarkin ya yi ƙawance da yayan kungiyar Ikhwanul Muslimun a daidai lokacin da suke tsaka da fuskantar matsi daga mahukuntan Misra da suka sanya musu ƙahon zuƙa a cikin kira da suke yi wajen tabbatar da bin tsarin Littafin Allah da sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi).

Haka kuma a shekarar 1962 da taimakawar takwarorinsa sarakunan Larabawa da Alhaji (Sir.) Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Arewa, ya kafa Majalisar Musulmin Duniya, wato Muslim World League, majalisar dake taimaka wa alumma da miliyoyin daloli a ko ina a faɗin duniya. (Rethinking Religion: The Legacy Of the US-Saudi Relationship Rachel Bronson (2005). The Washington Quarterly 28 (121-137) 8 April, 2012).

Haka kuma Sarki Faisal ne ya kafa Bankin Musulunci na Islamic Development Bank a shekarar ƙarshe ta rayuwarsa, 1975, wanda izuwa yanzu akwai ƙasashe har 56 a duniya da suke da hannun jari ciki har da Najeriya. (IDB Group In Brief. Retrieved 03 August, 2012)

A ranar 25 ga Maris, 1975 ɗan ɗan uwansa, Faisal bn Musaid bn Abdul’aziz ya kashe shi ta hanyar kisan gilla, kwanaki kaɗan bayan dawowarsa daga Amurka, wanda hakan ya sanya da yawan manazartan Musulmi tunanin cewa an shirya kisan na sa ne a can Amurka, wanda suke ƙyamatar ayyukan da yake yi na bunƙasa addini da kuma rashin amincewarsa da kafa tubalin samar da sabuwar Saudiyya da babu ruwanta ko take da sassauci a ɓangarorin addini.

Sarki Faisal ya rasu a asibiti ranar 18 ga Yuni, 1975 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Bayan rasuwarsa iyalansa sun kafa gidauniyar tunawa da shi King Faisal Foundation. Daga cikin ayyukan wannan gidauniya har da ba da kyautar girmama wa King Faisal Award ga fitattun mutanen da suka bada gudunmawa wajen ci gaban addini da rayuwar alummar Musulmi. Cikin waɗanda suka karɓi wannan kyauta har da Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi a (1992), da Sheikh Ahmad Lemu daga Najeriya da sauran mutane masu yawa.

Ina roƙon Allah Ya ji ƙan Sarki Faisal ɗan Abdul-Aziz, Allah Ya saka masa da mafificin alheri bisa ayyukan da ya yi wa Musulunci, Allah Ya shiryi shugabanninmu, Ya tsayar da su a kan tafarki madaidaici.

Aliyu Ibrabim Sani Mainagge malami kuma marubuci
Ya rubuto daga Kano
Za a iya samun sa a kan lambar waya: 08068985599, ko adireshin email:alibabapress2020@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan