Yadda Wa da Ƙani su ka haɗa baki su ka sace naira miliyan 70 a wani banki a Kano

206

Wasu ƴan gıda daya a jihar Kano, Yusuf Mukhtar da Bashir Mukhtar da ke aiki da Bankin GTB da kuma Babban Bankin ƙasa CBN, sun hada baki wajen sace naira miliyan 70 mallakar Bankin da kuma kona motar dake dauke da kudin domin boye shaida.

Jaridar Daily Nigerian ta ce mutanen biyu sun hada baki ne da direban motar wajen sace kudin da kuma cinnawa motar wuta ranar 13 ga watan Nuwamban da ya gabata a Jami’ar Bayero dake Kano.

Jaridar tace bayan sun cinnawa motar wuta da misalin karfe 6.47 na yamma, sun kwashe wasu kudaden dake ciki suka zuba a wata mota kafin isowar jami’an kashe gobara da ‘yan sanda.

Jaridar tace shaidu a Jami’ar sun tabbatar da ganin lokacin da aka sanyawa motar wuta da kwashe kudin kudin dake ciki, kamar yadda ta wallafa hotan bidiyon motar na cin wuta.

Direbar motar da aka kama, shi ya fara shaidawa ‘yan sanda abında ya faru, kafin daga bisani aka kama Bashir da dan uwansa, kuma tuni aka gano naira miliyan 40 a gidan mahaifinsu.

Rahotanni sun ce bayan kama mutanen an kuma sake su akan beli, ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba, yayin da Jaridar tace wata majiya ta shaida mata cewar an baiwa ‘yan Sandan naira miliyan guda da rabi domin sakinsu.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da kama wadanda ake zargi, inda yace yan sanda na cigaba da gudanar da bincike.

Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan