Lokaci yayi da gwamnatin tarayya za ta ɗauki ƙwararan matakai akan tsaro – Atiku Abubakar

152

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai domin kubutar da Najeriya.


Atiku Abubakar wanda shi ne ya yiwa jam’iyyar PDP takarar shugabancin kasar nan a zaɓen shekarar 2015, ya bayyana hakan ne jim kaɗan da ɓullar rahoton sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Sakandire da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara da ke jihar Katsina.


Sace Dalibai da aka yi masu yawa a makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara a jihar Katsina, abu ne dake nuna yadda matsalar tsaro ke kara fantsama a ƙasar nan, wanda dole ne ayi Alllah-wadai dashi da babbar murya”

“Yayin da kuma nake kira ga hukumomin tsaron wannan kasa da su dauki matakai cikin gaggawa domin ceto wadannan dalibai da aka sace”

“Kuman haka ina ganin ya kamata mu daina amfani da tsarin ihu bayan Hari, kan matsalolin tsaro, ya kamata a farga ayi wani abu”

Ya ƙara da cewa “A saboda haka nake kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta shelanta dokar ta baci a jihohin da matsalar tsaro ta dabaibaye, sakamakon ayyukan ta’addanci, domin kaddamar da gagarumin yaki kan ta’addanci da matsalolin tsaro”

“Domin kawar da kokonto, ya kamata dokar ta bacin da nake kira ayi, ta kasance karkashin kundin tsarin mulki na shekarar 1999, ta hanyar barin duk wasu tsare-tsaren mulkin dimukuradiyya a jihohin da kananan hukumomin da abin ya shafa, ba tare da an taba su ba”

“Manufar mai sauki ce, saboda akwai alamu ba rashin nasarar yakin da muke idan aka cigaba da amfani da salon da muke amfani da shi a shekaru biyar da suka gabata, domin a fili take, bai yi tasiri ba, musamman da aka sace wadannan yara na sakandaren Kankara”

“Idan muna son samun sakamako mai kyau, dole mu aiwatar da ingantattun tsare-tsare. Tsare-tsaren kuwa na iya zama harda dakatar da tsarin makarantun kwana na wani lokaci a wadannan jihohi, a koma makarantun jeka ka dawo, har zuwa lokacin da za a shawo kan alamarin”

“Sannan a girke jamian soji tsawon sa’o’i 24 a kowace makaranta dake wadannan jihohi”

Haka kuma Atiku Abubakar ya ƙara da cewa Babu wani abu da da ya dara zaman lafiya muhimmanci, domin dawo da doka da oda a garuruwan da abin ya shafa, kuma wannan ya kamata gwamnatin tarayya ta mayar da hankali akai har sai an kawo karshen wannan masifa.

A ƙarshe ya jajantawa al’ummar jihar Katsina bisa afkuwar wannan ibtila’i na sace ɗaliban da aka yi, tare da addu’ar Allah ya kawo ƙarshen wannan masifa.

“Ina jajantawa iyayen wadannan yara da aka sace da Gwamnati da al’ummar jihar Katsina, garina na biyu, kuma garin wanda nake mutukar girmamawa wato Tafida Shehu Musa Yar’adua. Ina addu’ar Allah Ya dawo mana da wadannan yara lafiya cikin aminci”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan