Duk Ɗalibin Da Muka Samu Da Maguɗi Ba Zai Sake Rubuta Jarrabawarmu Ba— WAEC
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta amince da hana ɗalibai da aka kama da maguɗin jarrabawa sake rubuta Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Afirka ta Yamma, WASSCE.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da WAEC ta fitar ranar Litinin bayan kammala taron ganawa da Kwamitin Gudanar Da Jarrabawa na WAEC ya yi karo na 70.
Kwamitin dai shi ne ƙololuwa a kan al’amuran da suka shafi jarrabawa da WAEC take shiryawa.
WAEC ta ce duk ɗaliban da aka kama da maguɗin jarrabawa za a hana shi sake zama jarrabawar na “tsawon wasu shekaru”.
Kwamitin ya kuma amince da ƙaƙaba takunkumi a kan dukkan nau’in maguɗi da ya haɗa da cire sunayen masu duba jarrabawa.