CITAD za ta horas da matasa 5000 yadda ake amfani da shafukan sada zumunta

14

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD da ke jihar Kano, ta bayyana ƙudurinta na baiwa matasa dubu biyar horo akan yadda za su yi amfani da shafukan sada zumunta wanda aka fi sani da ‘Social Media’, domin yaƙi da cin hanci da rashawa tare da ganin an tabbatar da adalci a hukumomi.

Babban daraktan cibiyar ta CITAD, Dakta Y. Z Ya’u ne ya bayyana haka a lokacin wani ƙwarya -ƙwaryan bikin ƙaddamar da ɗakin bincike na musamman akan shafukan sada zumunta tare da gidan radio mallakin cibiyar da zai dinga yaɗa shirye-shirye sa a shafukan Intanet.

Dakta Y. Z Ya’u ya ce la’akari da ɓullar shafukan sadarwa na intanet, hakan ya bayar da ƴancin faɗar albarkacin baki wanda kuma ya zama wajibi ƴan Najeriya sun san yadda ake shugabantarsu, ta hanyar tofa albarkacin bakinsu a shafukan na intanet.

Ya ƙara da cewa shafukan na sadarwa na zamani wata kafa ce da al’umma za su bayyana ra’ayinsu, sai dai da yawan masu amfani da ita ba su san yadda za su iya faɗar ra’ayin na su ba. Ya ce babban maƙasudin da ya sanya cibiyar ta CITAD ta buɗe wannan ɗakin bincike na musamman akan shafukan sadarwa na zamani shi ne; domin horas da marasa wajen amfani da shafukan domin samar da sabuwar Najeriya mai cike da adalci da gaskiya

Haka kuma Dakta Y. Z Ya’u ya ce ita kuma gida radiyon za ta zama wata kafa da za ta dinga horas da ɗaliban da su ka karanci aiki jarida a manyan makarantu.

A nasa ɓangaren shugaban taron, Farfesa Muhammad Habu Fagge, malami daga jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana cewa shafukan sadarwa na zamani wani dandali ne da duniya ta ke yayi da iya zai haɗa mutum da wasu manyan ƙungiyoyi.

Farfesa Habu Fagge ya kuma yi kira ga masu amfani da shafukan sadarwar na zamani da su yi amfani da shi wajen bincike da faɗakarwa.

A nasa jawabin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Usman Bala Muhammad ya taya cibiyar ta CITAD murna akan samar da wannan gidan rediyo irin sa na farko a jihar Kano.

Hakazalika, kwamishinan ya ja hankalin da cibiyar da su yi amfani da gidan rediyo bisa tanadin tsarin mulkin Najeriya, domin kaucewa tuhuma daga mahukunta.

Cibiyar ta CITAD dai ta buɗe wannan gidan rediyo da ɗakin bincike na musamman akan shafukan sadarwa na zamani da tallafinn gidauniyar MacArthur.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan