Home / Kuɗi/ Tattalin Arziƙi / Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata naira dubu 20 a jihar Jigawa

Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata naira dubu 20 a jihar Jigawa

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bada jari ga matan karkara, inda mata dubu hudu da dari uku da hamsin suka amfana da shirin a jihar jigawa.

Ministar ma’aikatar kula da al’amuran jin-kai da annobar da kuma kyautata jin dadin jama’a, Hajiya Sadiya Umar Faruq ta sanar da haka lokacin kaddamar da shirin a babban birnin jihar wato Dutse.

Gwamnatin tarayya ce ta bullo da shirin domin cimma manufarta ta fidda yan Najeriya daga kangin talauci nan da shekaru goma masu zuwa.

Ministar wacce ta samu wakilicin babban sakataren ma’aikatar Nura Alkali ya ce kowace mace zata sami jarin dubu ashirin-ashirin.

Daga nan ya bukaci wadanda suka amfana jarin su yi amfani da shi wajen bunkasa sana’o’in su.

A nasa jawabin gwamna Muhammad Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin bunkasa tattalin arziki, Alhaji Abba Mujaddadi ya ce a nata bangaren gwamnatin jihar jigawa na tallafawa kudirin gwamnatin tarayya wajen rage fatara da talauci, inda daga shekara ta 2015 zuwa yanzu aka tallafawa matan karkara dubu goma sha hudu da sana’o’in dogaro da kai.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *