Me ke hana mata aure?

  229

  Mutane da dama sukan shiga damuwa idan har su ka ga mace ba ta da aure musamman Bazawara ba a taba tunanin ina matsalarta take mene dalili maimakon haka kazafi da sharri da kallon banza da tsangwama shi ne zai biyo baya in har ba a yi sa’a da dacen bazawarar kwarai ba sai ta fada wani yanayi marar dadi musamman ma idan ta yi jinkirin tashi. Mace ba ita kadai ce ke jinkiri ba, akwai maza da yawa sun ki aure amma su al’umma ta karbi uzirinsu tare da kawar da kai.

  Aure yarjejiniya ce tsakanin ma’aurata bisa sahalewar zukatan juna da amincewa. Duk macen kwarai tana fatan ta ganta cikin gidanta da mijin da ta zaba ko iyaye suka zaba mata don samun nutsuwa da samun iyali. Akwai dalilai da dama da mata a yau suke fuskata musamman matar da ta taba aure ta fito ko dai a sanadiyyar mutuwa ko kuma a sanadin mutuwar aure.

  Tarbar Fari Ta Iyaye:
  Iyaye da dama taryar da suke yi wa ‘yarsu lokacin da ta dawo gida aurenta yam utu daga nan take fara yanke kaua da dukkan farin ciki. Ba sa bambance sakin da mace ce ta ta yi gajen hakuri ko rashin gaskiya a ka sake ta a kansa da sakin da gajiya da tozarcin da namiji ne ya janyo shi. za a tsangwame ta a hadata da kannenta suma su dora akan tsangwamar iyaye sannan ayyukan gida duk ita ce ke da alhakin yin sa kuma ba ko sannu. kanne gwargwadon yadda uka fahimci rashin muhimmancinta a gidan gwargwadon rainin da za su taryeta da shi.


  Sabulun wanka da wanki da sauran kayan kyalekyalen mata ba me ba ta. Duk wani ’yanci da ta ke tuanin tana da shi da take gidanta yanzu babu shi da wanne za ta ji? Yayin da ta zama a hargitse ba nutsuwa a zuci babu a zahiri wanne namijin ne kuma zai kalleta da sunan zai kai gidansa?Tun daga nan an sama mata bizar zama a gida babu ranar tashi. tarairayarku da ba ta abin da take bukata dai-dai iko shi ne zai sa ta kauwame ta zama ba ta nema gun kowa kuma y aba ta damar nutsuwa da zaben miji na gari ba tare da gaggawar maza ta tashi ta huta ba inda da dama irin wannan ke haifar da da-na-sani


  Fargabar Mijin Baya:


  Bahaushe ya ce, “wanda maciji ya sara idan ya ga bakin tsumma sai ya gudu.” Mata da dama rashin dacen auren mijin baya sai ya tsaya musu a zuciya har ya janyo su yi wa maza kudin goro su shiga tsoron maza su yanke kauna da dukkan jin kai da ake samu gun namiji. Wannan hujjar mata kan rike sai su gwammace zaman gidan don a hangensu ya fi kwanciyar hankali da hutun matsala. Wanda wannan hangen mai rauni ne don ba duk maza suka taru suka zama daya ba cikinsu akwai na kirki da suke rikon aure kamar yadda ya dace. Mata da yawa Allah ya yi musu sakayya a sabon aure hark a ji mace na fadin ita sai yanzu ta san ta yi aure. Ala kulli halin bai wa Allah zabi shi yafi dacewa.

  Masu Zuwa da Zuciya Biyu:


  Sau tari iyaye da yan’uwa su kan ga mace ta ki aure ne kawai don ruwan ido ko don kwadayi ko kon son zuciya wasu ma in sun so yin fashin bakin da son zuciya sai ka ji a na cewa budurwar zuciya ce yaro take jira ka ji halin dan adam wasu daga gefe mace na bacci su suna yi mata numfashi da kazafe-kazafe. Abin da aka kasa ganewa wadannan da suke faman zarya da dama ba da niyyar auren suke zuwa ba kawai su a tunanin su tunda mace ta yi aure to tana da damar yin lalata asirinta ya rufu kuma a matse take sannan tana da dabarar kare kanta ga samun ciki don abin kunyar sai ya fi shafarta. Zawarawa da dama babban tashin hankalin da suke fuskanta kenan, amma ba a ganewa sai a bi su da mummunan zato.

  Matsalolin Yara:


  Mata da dama tausayi da kauna da jin kai na tsakanin uwa da da kan kawo musu tarnaki gun sabon aure. Mutane sun san matasalolin da ‘ya’yan riko ke fuskanta ko dai in aka yi rashin sa’a matar uba ta hana su gudanar da rayuwarsa ta yadda ya dace maimakon haka ma sai ta bige da azabtar dasu nau’ikan azaba ko mahaifin da aka bar wa ya yi ko in kula da rayuwarsu inda dai a karshe za su tashi da gurbatacciyar rayuwa. Shi kuwa sabon miji ba zai yarda a kai masa agola ba ko da kuwa ya karba ba inda ake zuwa abin yake lalacewa. Wannan na zama gagarumar matsala ga mace wadda in ba wadda ta kai zuciya nesa ba da wuya ta iya rufe ido ko da kuwa ta yi wani auren hankalinta na gidan da ta bari wajen yaranta.

  Rashin Abin Yi:


  Daga cikin matsalolin da ke saw a aure yam utu da dam aba sa ketare wannan ajin ko dai saboda rashin abin yi da tattalin arziki ta buwayi miji da ba ni –ba ni ko kuma saboda an yi mata kishiya in ma an yi rashin dace wadda ta fi ta ilimi ko yarinta ko kuma abin hannu. Wannan sai ya tunzura mace kan ita ma ba za ta kuma wani auren ba sai ta samo abinda a ka nuna mata yatsa kansa. Garin neman cike wannan gibin sai a dau lokaci duk na kirkin da suka zo a tankwabar a karshe abin da ake nema ya zo hannu amma ba mijin ko kuma ma a yi biyu babu ba mijin ba burin. Maimakon haka kamata ya yi ake sara ana duban bakin gatari mijin kwarai bai gaba da karatu da ci gaban mace don haka a hanyar cikar buri in aka sami na kwarai sai a shiga daga ciki a karasa.

  Kallon-kallo:


  Sau tari mata musamman wadanda suka taba aure suna kallon kansu a masu cikakken ‘yanci don haka suna da zabinsu don gina rayuwar da suke shirin shiga gaba. Inda rashin sa’ar ke zuwa, su mata mazan da suke hange su suka dace da rayuwar da suke shiri a daidai wannan lokacin wadannan mazan ba da gaske suke ba yaudara ce a zuciyarsu su kuma wadanda suke sonsu tsakani da Allah matan hankalinsu ba ya kansu don suna yi musu kallon ba su cike sharuddan da suke nema ba. Akwai kuma mata da suke aiki ko suke wata sana’a ko iyayensu ke da hali ko mace mai ilimin da ta taka wani matsayi maza kan ji tsoron tunkararsu duk kuwa da nagartar su mazan sun manta da Bahaushe ya ce a rashin kira karan bebe ya bat aba a san inda za a dace ba maimakon tsoro kamata ya yi namiji ya nemi kyakkaywar hanya ta tunkarar wadda yake so in har ya san son gaskiya ne ba yaudara ko kwadayi ne ba. Haka babban kuskure ne kin auren wanda yake sonki ya shirya zama da ke don Allah. Ki auri wanda ya nuna da gaske yake sonki ya fi miki alkhairi kan hangen wanda bai zo hannu ba bai ma shirya zama da ke ba.

  Ruwan Ido:


  Wata kuwa matar ruwan ido da hange ko dai mijinta na baya mai sukuni ne don haka duk dogon zama za ta jure kada ta ci baya a yi mata dariya wata kuwa ita take kallon kanta a matsayin wata da dole mijin da za ta aura sai misalign irin su wane ko mai kudi wane ko dan siyasa da sauran irin wadanda suke gani ko ji suna da wani madafun iko. wata ma daga gidan talakan ta fito amma ko iyayenta ba ma su halin ba ne amma sai ta dauki son abin duniya ta dorawa kanta hujja kadai saboda al’umma su ga ta ci gaba. Mata kan manta kwanciyar hankali da fahimtar juna ya fi tulin arziki. Haka arziki na Allah ne shi ke arzurta bawa ta inda ba ya zato.

  Addu’a:


  Duk bayan an bi matakai babban matakin nasara a rayuwa shi ne addu’a gaggawa a aure ba ita ce mafita ba ruwan ido da kure dukkan matakan iya zaben miji ba shi ne nasara ba,addu’a da mikawa Allah zabi da neman dacensa da ikhlasi yayin da za a zabi miji shi ne kwanciyar hankalin mace. Yayin da kuwa aka ga wani abu da ba a fahimta ba a tsaya a gane shi in har da matsala a hakura tare da fauwala wa Allah shi ya fi in kuma ya samu a godewa Allah a kara dagewa da addu’ar tabbatarsa
  Allah ya kawo wa mata dauki da wannan tsaka-mai wuya da suke ciki na neman ina mijn kwarai yake su aura.

  Bilkisu Yusuf Ali Malama Ce A Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Jihar Katsina, Ta Rubuto Daga Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan