Boko Haram: Turawa Sun Taimaka Wa Borno Fiye Da Larabawa— Zulum

146

Ƙasashen Turawa sun fi taimaka wa jihar Borno a kan rikicin Boko Haram da yake ci gaba da addabar jihar, fiye da ƙasashen Larabawa da suke da al’adu da addini irin na mutanen Borno, a cewar Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum.

Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi baƙuncin Jakadan Ƙasar Falasɗinu a Najeriya, Saleh Fheied Saleh a Fadar Gwamnatin Jihar, Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa Falasɗinu a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Larabawa da ta sha bamban da ‘yan uwanta.

“Ni mutum ne mai son yin komai a aikace. Nakan yi aiki da zahirin abinda na gani a ƙasa. A tsawon shekarun da muke fuskantar ƙalubalen tsaro, mun samu tallafin jin ƙai daga Birtaniya da sauran sassan Turai, Amurka, Kanada, daga Jafan da sauransu da dama waɗanda suka nuna damuwa suka kuma yi ƙoƙari wajen taimakon al’ummarmu da suka shiga damuwa ta hanyoyi da dama da suka haɗa da abinci, magunguna da kudade.

“Amma irin wannan taimako bai zo daga ƙasashen Larabawa ba, ƙasashen da suke da al’adu da addini irin na miliyoyin al’ummar Borno. Muna da ‘yan asalin ƙabilar Shuwa Arab a Borno, wannan kuma yana nuna tarihinmu yana da alaƙa. Mun yi ƙoƙari sosai, mun rubuta takardu tare da ziyartar ofisoshin jakadancin ƙasashen Larabawa, musamman waɗanda suke da arziƙi kuma ba sa cikin yaƙe-yaƙe, amma a gaskiya, mafiya yawan Larabawa ba su damu da halin da muke ciki ba, kuma ba sa tallafa mana.

“Larabawa ba su nuna damuwarsu gare mu ba. Amma ziyararka ta sabunta fatanmu musamman, kuma mun gode maka sosai da ziyararka”, in ji Gwamna Zulum.

Jakadan na Falasɗinu ya sanar da Gwamna Zulum wani shiri na tallafa wa Gwamnatin Jihar ta Borno a wasu wurare da take da buƙata.

“Akwai kamfanonin Falasɗinu da yawa a Najeriya, a shirye suke su yi aiki da Gwamnatin Jihar Borno, a shirye muke mu haɗa kai da ku, a shirye muke mu taimaka muku a kan duk wani da kuke so mu yi wanda za mu iya”, in ji Jakada Saleh.

Jakadan ya kuma ce akwai ‘yan Najeriya da dama da suke zaune a Falasdinu a halin yanzu, musamman ‘yan jihar Borno, wasu ma daga cikinsu sun hidimta wa gwamnati da al’ummar Falasɗinawa.

Ya bada misali cewa a cikin al’ummar Borno da suke Falasɗinu, akwai wata mata da ake kira Fatima Barnawi, wadda ta taɓa riƙe muƙamin minista da ma na ‘yan sanda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan