Har yanzu bamu shirya komawa makaranta ba – Ɗaliban Jami’ar Bayero

197

Wasu daga cikin ɗaliban jami’ar Bayero da ke Kano, sun bayyana cewa ba lallai ne su koma karatu ba a wa’adin da hukumomin jami’ar su ka ambata ba.

Wannan dai yana zuwa kwana ɗaya da hukumar gudanarwar jami’ar ta ambata ranar 18 ga watan Janairun nan a matsayin ranar da ɗalibai za su koma bayan shafe watanni tara da Malaman jami’ar su ka shafe suna yajin aiki.

Wasu daga cikin ɗaliban da su ka tattauna da manema labarai sun bayyana cewa har yanzu ba su kai ga kammala shirya komawa makarantar ba.

Al’ameen Usman Abubakar na ɗaya daga cikin sababbin ɗaliban da su ka samu gurbin karatun digiri na biyu a tsangayar harkokin aikin jarida da sadarwa ya bayyana cewa bai yi zaton ɗaliban karatun digiri na biyu za su dawo akan lokaci ba.

Al’ameen Usman ya ƙara da cewa duk da cewa hukumar gudanarwar jami’ar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairun a matsayin ranar komawa harkokin karatu, amma shi bai yiwuwar hakan ba domin har yanzu bai kai ga kammala biyan kuɗin makaranta ba sakamakon yajin aikin da aka yi ta fama da shi.

Shi ma a nasa ɓangaren Aminu Muhammad da ya samu gurbin karatu a tsangayar halayyar ɗan adam ya yi ƙorafin cewa sa a makon jiya ya samu damar shiga shafin jami’ar domin yin rijista, wanda kuma har yanzu bai kai ga kammalawa ba.

Aminu Muhammad ya kuma yi ƙorafin cewa lokacin da hukumomin jami’ar su ka bayar ya yi matuƙar kaɗan.

Shi ma Kamaluddeen Muhammad, wanda ke sashen koyon aikin Injiniya ya bayyana cewa yana matuƙar fargabar ranar komawar domin a halin da ake ciki da yawa bai san inda kayan karatunsa su ke ba. Ya ƙara da cewa duk da cewa yana cike da farin ciki da ranar dawowar, amma zai sha wahala kafin ya iya dawowa yadda ya kamata.

Ita kuwa Hasiya Abubakar, ɗaliba a sashen kimiyyar haɗa ilimin sinadarai ta bayyana cewa ranar dawowar ta zo mata a bazata duk da cewa ɗalibai sun gaji da zaman kashe wandon da su ke yi.

Hasiya Abubakar ta ce hutun annobar Korona da kuma dogon yajin aikin da aka yi fama da shi ya sanyayawa mafi yawan ɗalibai gwiwarsu akan harkokin karatu. Ta ƙara da cewa abu ne mai wahalar gaske ta iya barin harkokin kasuwancinta ta mayar da hankalinta akan darussan da ake koya musu, domin jadawalin karatun da jami’ar ta fitar sun nuna mako biyar kacal za a yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan