Murnar Cika Shekara 58: Mahaifiyar Abba Kabir ta ba shi kyautar alƙur’ani

244

Mahaifiyar tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabiru Yusuf mai laƙabin Abba Gida – Gida ta ba shi kyautar alƙur’ani mai girma.

Kyautar Alkur’ani mai girma din ta zo ne a dai-dai lokacin da Abba Kabiru Yusuf ya ke cika shekaru 58 da zuwa duniya wanda kuma yayi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar tasa cikin iyalan gidansu.

Tun da farko Mahaifiyar Abba Gida – Gida, Hajiya Khadija Kabir Yusuf, ta gabatar masa da kyautar Alƙur’ani mai girma a matsayin kyautar taya murnarta a gareshi tare da dafa kan sa ta sanya masa albarka sannan tayi masa addu’ar kariya daga Allah.

Tuni dai hotunan kyautar Alkur’anin ya fara karaɗe Shafukan sadarwa na zamani, inda al’umma ke tofa albarkacin bakinsu.

Addini dai yana da matuƙar tasiri a siyasar jihar Kano, hakan ce ta sanya masu neman mulki a jihar ke dangantaka kawunansu da masu bin dokokin addinin musulunci sau da ƙafa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan