Ƴan Hisba a Kano sun kama maza da mata tsirara a lokacin da su ke aikata alfasha

639

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama maza da mata guda 53 tsirara suna aikata alfasha da ta’ammali da miyagun kwayoyi a unugwar Lamido crescent da ke karamar hukumar Nasarawa a nan Kano.

Babban kwamandan hukumar Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba.

Ibn Sina ya ce cikin wadanda aka kama akwai maza 27 da mata 26 duk kuma suna da matsakaitan shekaru

“Waɗanda ake zargin sun hada da maza 27 da mata 26, kuma dukkansu‘ yan tsakanin shekaru 17 zuwa 19.

“Mutanenmu sun je wurin da misalin karfe 10:00 na dare sannan mun cafke mutum 53 da ake zargi”

Ya kara da cewa cikin wadanda ake zargin an kama wasu tsirara suna lalata a bandakuna da gefen titi.

A ƙarshe Ibni Sina ya ce hukumar ba za ta saurarawa ɓata gari ba a faɗin jihar Kano tare kuma da yin gargadi ga matasa da su guji aikata munanan laifuka tare da zama jakadu nagari.

Kano Focus

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan