Ƴan majalisa na shirin yin dokar halatta noman tabar wiwi a Najeriya

623

Ƴan majalisar wakilai na Najeriya na yunkurin yin dokar da za ta halasta nomawa tare da kasuwancin Wiwi domin magani da yin kayan kwalliya da bincike da kuma samar da kudaden shiga.

Wannan na kunshe ne cikin wani da kudiri na daidaita amfani da Wiwi da Miriam Onuocho, ta gabatar a 2020, wanda ke jiran karatu na biyu a majalisar.

Idan za a iya tunawa a cikin shekarar 2014 sai da hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya ta ce Najeriya ce tafi kowace kasa yawan noma ganyen wiwi a Africa.

Hukumar ta bayyana hakan a yayin gabatar da rahoton ta a gaban hukumomin yaki da miyagun kwayoyi da magunguna da abinci a Najeriya.

Haka kuma a cikin shekarar 2019 sai da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da shugaban hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA, Muhammad Mustapha Abdallah su ka kai ziyara ƙasar Thailand domin sanin yadda ake shuka Ganyen Tabar Wiwi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan