Home / Labarai / Babu dalilin da zai sanya in sasanta da ƴan bindiga – Abubakar Sani Bello

Babu dalilin da zai sanya in sasanta da ƴan bindiga – Abubakar Sani Bello

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce ba zai yi ko wacce irin sasantawa ba da ‘yan bindigar da suke ‘ta’addanci’ ba a jihar.

Abubakar Sani Bello ya yi wannan kalamai ne lokain da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala wata tattaunawa da ya yi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadar shugaban da ke Abuja, game da ƙaruwar matsalar rashin tsaro da kuma lalacewar ababan more rayuwa a jihar.

Gwamnan ya ce ya dakatar da duk wata dama ta tattaunawa da waɗannan ‘yan bindiga, saboda ba sa tsayawa kan alƙawarinsu, domin a baya ya taɓa yin irin wannan yarjejeniya da su kuma ba ta kawo wani sauyi ba.

Bello, ya ce a kwanan nan jihar na fuskantar tururuwar ‘yan bindiga waɗanda suke shiga ta kan iyakar Jamhuriyar Benin, yana mai cewa ” Fulani ne waɗanda ba su da mai fada musu su ji ko da iyayensu ne.”

Ya kuma ce matsalar ‘yan bindiga ita ce ta fi damun gwamnatin jihar a yanzu.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kama wasu dagattai sakamakon zargin su da haɗa kai da ƴan bindiga domin aiwatar da hare-hare.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Yadda aka yi addu’ar cikar Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa shekara 1 a kan mulki

Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *