Hukunci da hujjoji akan ta’amuli da POS a mahangar Islam

199

Wasu mutane sun dauka abunda ba su fahimta ba shine Shubha a addini, saboda haka idan an gaya musu hukuncin Shariah wanda basu san shi a baya ba sai su ce Shubha ce. Ita kuma Shubha daban jahiltar Abu daban.

Zan kawo bayanai daki-daki kuma kowanne da hujjar sa, kalubale ne na ilimi ga Almajirai da Malamai kowa ya yi iya binciken shi da nazari, duk wanda yake son warware bayanai na dole ya kawo hujjoji na kai tsaye kamar yadda na kawo. Idan mutum ba zai iya kawo hujjoji ba, to kar yayi girman kai ya sallama kawai a wuce wurin.

Ba kowanne mutum ne dan ya iya karatun larabci ko ya zama Malami mai waazi ko Almajiri mai zuwa darasi yake da ikon tattauna mas’alar Fiqhun addini ba, shi fiqhu fanni ne na ilimi da dole sai mutum ya karanci abubuwan da suka shafe shi kamar; ma’ani ayaatul qur’an, ilmul-hadith walmusdalahat, usulul-fiqh, qawa’id al-fiqhiyya, ilmul-lugha, ilmul muqasid wal mustajiddaat d sauran su, sannan yayi bayani akan mas’alah ta fiqhu.

Idan kun kula ban ce ilmul Quraan ko Qiraa’at ko hadith ko fiqhu ba, domin sanin wadannan zai mai da kai masani ne amma ba mai bada fatwa ba, ko a zamanin su Imam Malik akwai Malamai, amma ba su zama fitattun ma su bada fatwa ba. Saboda haka abun yana da ka’idoji. Ba haka sakakai kawai idan mutum ya hau mimbari shikenan sai ya halalta ko ya haramtawa mutane abu kamar ya zama sabon al-shari’u ba.

Misali akan maganar da muke yi kwanannan shine Riba a kasuwancin POS. Idan mutum yana so ya fahimci wannan hukuncin zai duba ne, menene manufar ma su POS, kuma wanne aiki ma su POS ke yi, sannan menene illar haramta shi, kuma menene sakamakon da zai faru idan Musulmi suka haramtawa kan su shi.

1- Farko asalin ma su POS ba su taba ayyana shi cikin interest din banki ba, yana cikin “services” ne. Anan ka’idar الأمور بمقاصدها za ta yi aiki.

2- na biyu mai POS yana biyan kudi ya sayo gadget, ya je banki ya karbi kudi, domin ya biyawa “customers” din shi bukata a saukake, tayaya zai baka kudi kyauta saboda kai Musulmi ne? Anan ka’idar الخراج بالضمان za ta yi aiki.

3- sannan mai amfani da POS yana samarwa kan shi saukin kudin mota, bin layin ATM, da kuma biyan bukatar shi cikin gaggawa, Don me ba zai biya ba? Anan ka’idar الغرم بالغنم za ta yi aiki.

4- idan dukkan Musulmi suka kauracewa POS za su sha bakar wahala, kuma bankuna za su fara kyamar mu’amala da su, dalilin haka sauran al-umma za su yi musu zarra wajen kasuwanci. Anan Kaidar مالا يتم الواجب إلا به فهو واجب za ta yi aiki.

5- Sannan idan har dagaske ne POS ya zama Riba to Musulmi dukkan su yan’wuta ne khalidina fi ha. Anan Kaidar المشقة تجلب التيسير za ta yi aiki.

Wannan duka hujjoji ne, saboda ba’a bayanin hukunci a Shariah sai da hujja ta ilimi, kuma mutum ba zai karanto ayar Qurani ko Hadisi sannan ya fassara cikin son rai, ko rashin sani ko karancin fahimtar sa ba, sannan ya tilastawa mutane su bi shi ba. Ba haka ake lamarin Fiqhun Addini ba.

Nema Afuwa: Ayi mun uzurin rashin daukar lokaci domin bayanan wadannan ka’idoji na fiƙhu ba, amma na kan koyar da dalibai su a Aji, a jamiar jihar Yobe, wanda ke son fahimta sosai, mu hadu a class.

Dakta Sheriff Almuhajir, Babban Malami ne a sashen addinin Musulunci na jami’ar jihar Yobe

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan