Ina kira ga majalisar dokokin jihar Kano ta binciki maganar gidan Zakka – Sa’idu Ahmad Dukawa

216

Fitaccen mai yin sharhi akan al’amuran da su ka shafi siyasa kuma malami a sashen koyar da kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya buƙaci majalisar dokokin jihar Kano da ta binciki batun da ake na cewa gwamnatin jihar Kano tana shirin sayar da gidan Zakka.

Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya yi wannan kiran ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na facebook, mai taken;

“GAME DA “MUHIMMAN WURARE DA AKE ZARGIN GWAMNATIN KANO DA CEFANARWA”
SHIMFIDA
A ranar Litinin 4/1/2021 ne BBC Hausa ta wallafa wani labari mai taken Muhimman Wurare da ake Zargin Gwamnatin Kano da Cefanarwa. An kasa wadannan wurare gida uku, kamar haka:

 1. Wadanda ake zargin cefanarwa baki daya, wadanda suka hada da
  a. Kamfanin Gidan Jarida na Triumph
  b. Filin fakin na Shahuci
  c. Otel din Daula
 2. Wadanda ake zargin siyar da wani sashe na su, kamar
  a. Makarantun Sakandare
  b. Filin wasa na Sabon Gari
 3. Wadanda ake zargin ana shirin sayarwa, sun hadar da:
  a. Gidan ajiyar namun daji (Zoo)
  b. Gidan Zakka.
  A daren Litinin din kuma na 4/1/2021, sai na ji daya daga cikin ‘yan Midiya, wanda na san yana harkar midiya da tsabta, ya koka game da gidan zakka, a wani shirin siyasa mai taken “Harshenka Alkalinka” na Rahma Radio tashar FM, har ma ya ambaci wasu daga cikin manyan mutane a Kano wadanda suka hadar da Babban Limamin Kano, kuma Farfesa Gangaran, Muhammad Sani Zahradeen da Kwarrarren Likita, kuma shugaban Hukumar Kula da Likitocin Najeriya, Farfesa Musa Muhammad Borodo.
  Saka gidan Zakka a cikin jerin wuraren da ake zargin gwamnati da shirin sayarwa shi ya sa na ga wajibcin yin bincike akan lamarin, saboda a iya sanina gidan Zakka wanda yake a Goron Dutse ba mallakar Gwamnatin Kano ba ne, wakafi ne da wasu bayin Allah suka samar don a yi aikin tattara zakka daga mawadata da rabawa ga mabukata.
  Sakamakon bincikena ya tabbatar min da cewar harabar gidan Zakka yana daga cikin wuraren da Gwamnatin Kano ta ke shirin sayarwa. Amman bayanin da na samu ba gidan Zakkar za a sayar ba, filin gidan da yake kewaye da shi za a sayar. Sannan na samu labarin wasu dattawa a Kano da suka hada da wadanda sunansu ya gabata da karin Farfesa Ibrahim Halilu Umar (tsohon Shugaban Jami’ar Bayero kuma tsohon shugaban Hukumar Zakka a zangon Gwamna Shekarau na biyu), da kuma Alhaji Kabiru Sani Hanga (tsohon Babban Darakta a Hukumar Zakkah, shi ma lokacin gwamnatin Shekarau) sun samu ganawa da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akan maganar. Sun bukaci da ya dubi Allah kada ya gutsure filin gidan Zakka. Sun yi masa bayanin tarihin gidan.

TAKAITACCEN TARIHIN GIDAN ZAKKA

Asali dai a shekarun 1980 Gwamnan Kano na farko na farar hula, Marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya bayar da filin ga wata al’umma da ta bukaci a bata don ta gina waƙafi ta siffar wata ma’aikata wacce zata rika karbar zakka daga mawadata tana rabawa ga mabukata. Ba a samu wadatar kudin da za a yi ginin ba sai a shekarar 1990 wani attajiri ya bayar da abinda aiki ya kankama, da wasu suka gani su ma suka saka tasu gudunmawar. Tun sannan ake yin wannan aiki na al’umma, kamar yadda addinin Musulunci ya bukaci a yi.
A shekarar 2003, da Malam Ibrahim Shekarau ya zama Gwamna sai ya kirkiri wasu hukumomi guda uku, ta Shari’ah, da ta Hisbah da kuma ta Zakka. Gwamnatinsa ta baiwa hukumomin Shari’ah da na Hisbah mahalli amman ta bukaci Hukumar Zakkah ta yi anfani da gidan Zakka a matsayin ofishinta. Wasu daga cikin Malamai har sun kyamaci yin hakan saboda kada wata rana wata Gwamnatin ta dauka gidanta ne ta sarrafa shi sabanin yadda aka assasa gidan, amman wasu suka kore wannan tsoron ta hanyar bada shawarar a yi ka’ida da sharuda a rubuce. Hakan kuwa aka yi.

Da aka samu sauyin gwamnati a shekarar 2011 Gwamna Kwankwaso ya nada Malaman da za su rike masa Hukumar Zakka, aka sanar da shi wannan sharuda ya amince da su. A shekarar 2015 da Gwamna Ganduje ya nada masu kular masa da harkar Zakka aka sake tunasarwa game da sharudan, aka amince.

A zangon Gwamna Ganduje na biyu sai aka samu sabani tsakanin lauyan da yake kula da gidan Zakka da Ma’aikatan gwamnati da suke gidan wadda har ta kai ga lauyan ya garzaya Kotu ya nemi da Ma’aikatan su tashi daga gidan, Kotu ta amince da bukatarsa. Bayan da Ma’aikatan gwamnati suka tashi sai ta dirarwa wajen ta fitar da abinda a Turance ake kira “curve out” (watau gutsire filin gwamnati a mallakawa wasu mutane). Wannan ce ta saka dattawan da na ambata a baya suka yi takanas-ta-Kano suka gurfana gaba ga Gwamna suka nemi alfarmar idan har sai an gutsire filin to a barwa gidan Zakka wanda yake fuskar gidan don kada a shigar da shi lungu mutane su manta da shi; kuma Gwamna ya amsa musu rokonsu a gaban idonsu. Amman da ma’aikatan gwamnati suka tashi fitar da feguna sai suka yi watandar dukkan filin ba tare da la’akari da alkawarin Gwamna ba.
Wannan shi ne dan takaitaccen tarihi da na iya samu game da gidan Zakka na Goron Dutse a Kano.
TSOKACI
Ba ya cikin dabi’ata na yi magana akan abinda gwamnati take yi a hukumance. Na fi yin magana akan abubuwan da ake yi a siyasance. Babban dalilina shi ne sanin da na yi cewar sau da yawa ayyukan hukuma suna haduwa da tirjiyar jama’a, alhali yinsu shi ya fi kyau, kuma sau da dama kyawun yana bayyana daga baya. Abubuwan kuma da rashin alfanunsa ya cancanci a yi magana akansu sau da yawa wasu kungiyoyi wadanda nake ciki suna magana akansu, don haka bana ganin bukatar na yi magana daban da wadda kungiyoyi suka yi. Amman akan gidan Zakka naga bukatar na magantu.

Da farko dai ina cikin wadanda Allah ya kaddarawa yawan kiraye kiraye akan al’umma su waye da samar da
wakafi don magance matsalolin talauci. Wakafi yana saukakawa al’umma har ma da gwamnatocinsu wajen magance talauci wanda yake zama barazana ga tsaro da zaman lafiya. Sai gashi misali daya tal na wakafi wanda ya wanzu tsawon shekaru masu yawa yana fuskantar baraza. Ba abin mamaki ba ne idan aka gama gutsire filin gidan Zakka aka hari gidan dungurungun! Don haka akwai hakki akanmu na mu fito mu yi magana don kare hakkin wadanda suka bada dukiyarsu don a taimaki al’umma.

Abu na biyu, duk da cewar gwamnati tana da ikon yin abinda ta ga dama da fili bisa dokar kasa, amman sanannan abu ne cewar doka ta bada wannan ikon ne kawai saboda a karewa al’umma abubuwa masu amfani a tattare da su. Don haka sabawa doka ne a gutsire filin al’umma, kamar na filin makaranta, ko na asibiti, ko ma filin wasa, a yi wani abin daban da ba na al’umma ba, kamar a sayarwa da daidaikun mutane. Kai hasali ma ba ya cancanta a maye wani abin na al’umma da wani na al’umma din; kamar a maye makaranta da asibiti, ko mayar da gidan Zakka ya koma gidan Marayu. Sai gashi kuma gidan Zakka ba ma na gwamnati ba ne amman ake zargin an sayar da harabarsa ga daidaikun mutane. Wannan ma dalili ne da zai sa dole mu yi magana.

Abu na uku, sau da yawa muatane suke kokawa cewar hukumomi suna aiwatar da abubuwan cutarwa ga jama’a amman manyan gari sun yi shiru, wani lokacin ma har jama’u akan yi, ace “kowa ya yi shiru!!!” A wannan karon sai gashi dattawan gari sama da biyar sun hadu sun gana da Gwamna amman an yi shakulatin bangaro da bukatarsu, kuma bukatar nan tasu ta al’umma ce. Magana ce fa guda daya: idan har gwamnati za ta baiwa wani fili a harabar Hukumar Zakka me zai hana ta mallakawa Hukumar ta Zakka filin ta bukaci ta raya shi saboda al’umar Annabi (SAW)? Babu shakka wadanda su ka yi dattaku irin wannan sun cancanci duk wani mai kishin al’umma ya goya musu baya. Don haka ina goyon bayansu, akwai bukatar gwamnatin Kano ta sake duba wannan bukatar.

Amman fa game da gutsire-gutsiren filaye a Kano, ba gwamnati ce kadai da laifi ba. Suma wadanda suke lalubo duk wani dan sarari da al’umma suke anfana da shi su ruga ga gwamnati su bukaci a mallaka musu suna cutar da gwamnatin, baya ga cutar da al’umma da suke yi. Kuma abin ya kara muni da abin nasu ya kai ga cin iyakar abinda aka samar da shi da sunan Allah (SWT), domin wakafi umarni ne na Allah (SWT). Don haka akwai bukatar su ma a yi musu gata a ceto su daga hatsarin da suke kutsa kansu a ciki. Akwai bukatar a ja hankalinsu, idan sun ki ji a taka musu burki. Don haka maganar ta wajaba.
Dalili na karshe da zan takaita akansa na bukatar na yi magana, shi ne yadda nake tsaye akan lallai kada mu yarda da masu bukatar cire hannun gwamnati daga mallakar kasa, kamar yadda wasu ‘yan rajin sauya fasalin kasa (restructuring) suke da buri. Na san ba abin mamaki ba ne idan wasu suka kalubalanceni cewar gashi nan ina daurewa gwamnatoci gindi game da a bar ikon mallakar kasa a hannunsu, yanzu tun ba a je ko ina ba ina kokawa da halayyar wata gwamnatin. Anan ina son na jaddada matsayata cewar a bar mana dokarmu yadda take. Na farko dai barnar da zata biyo bayan cire hannun gwamnati sai ta fi wacce muke kuka da ita a yanzu. Na biyu kuma a yanzu sabawa doka wasu suke yi tare da sabawa shawarar masana wajen yin abinda suke yi, kuma ba ma fatan hakan ta dore. Da yardar Allah idan ana tunasar da su, wata rana za su ji magana, idan ba su ji ba kuma wata rana za a samu masu ji su karbi ragamar mulki.
Wasu kuma suna kokawa game da tsarin dimokaradiyya saboda halayyar gwamnoninmu. Amman fa a sani tsarin dimokaradiyya ya tanadi yadda za a takawa gwamnoni birki idan sun tasarma ba daidai ba. Abinda da ya sa ake da Majalisun jihohi kenan. Don haka mutane su dage da shiga Majalisun jihohi kuma masu zabe su rika sanin wadanda za su zaba.
KIRA NA MUSAMMAN
A karshe ina kira ga Majalisar Jihar Kano ta binciki maganar gidan Zakka ta nemi Gwamna da ya saurari Dattawan da suka je masa ya dada fahimtar maganar kuma ya yi abinda ya fi dacewa. Wannan shi ne abinda zai taimake shi, ya taimaki gwamnatinsa, ya taimaki jam’iyyarsa, ya taimaki duk wani mai burin yin takara a karkashin jam’iyyarsa. Mafi muhimmanci kuma, tserar da gidan Zakkar nan shi ya fi kusa da taimakawa al’umma akan sayar da harabarsa ga wasu daidaikun mutane. Ko da za ace akwai wani abu na tsami tsakanin wakilan gidan na yanzu da jami’an gwamnati na yau, a karshe dai dukkanninsu masu shudewa ne wasu daban su zo. Wakafi kuwa so ake yi ya dore har illa ma sha Allahu!
A matsayinmu kuma na ‘yan Africa, wani lokacin mun fi tasirantuwa da alakar kusanci, ko ta jini ko ta srukuta ko ta auratayya ko ta abokantaka, fiye da tasirantuwa da dokar aiki. Don haka, ina rokon duk wanda ya san maganarsa tana da tasiri akan Gwamna Ganduje ya taimaka ya roke shi ya kawar da kai daga gidan Zakka; kai ya ma taimaka a kara fadada shi ta hanyar kara masa gine-gine da za su rika samar masa da kudin shiga.Yin haka zai zama ainihin hidima ga musulunci, sabanin yadda mutane za su fahimci al’amarin a matsayin cin zarafin addini da ake neman yi ta hanyar cefanar da filin gidan Zakka.
Allah ya sa wannan ‘yar gajeriyar nasihar ta fada kunnen da zai amfana da ita

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan