Ya Kamata A Riƙa Yi Wa ‘Yan Siyasar Najeriya Gwajin Ƙwaƙwalwa— Ganduje

155

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai buƙatar Majalisar Dokokin Najeriya ta yi wani ƙuduri da zai tilasta a riƙa yi wa ‘yan Najeriya masu neman muƙaman siyasa gwajin ƙwaƙwalwa.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne ranar Alhamis yayin raba tutoci ga ‘yan takarar ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

“Sakamakon bin tsarin gwada ‘yan takara da aka yi na shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, an samu waɗanda ke shaye-shaye a cikin ‘yan takarar.

“Jihar Kano za ta ci gaba da bin wannan tsarin domin tabbatar da al’umma ba su zaɓi wanda ke shaye-shaye ba”, a cewar Gwamna Ganduje, kamar yadda Gidan Rediyon Dala FM dake Kano ya rawaito.

Gwamnan ya kuma yaba wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, bisa yadda ta gudanar da aikin gwajin ‘yan takarar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan