Aminu Waziri Tambuwal ya cika shekaru 55: Me ku ka sani game da shi?

109

An haifi Aminu Waziri ranar 10 ga watan Janairun 1966 a kauyen Tambuwal da ke jihar Sokoto.

Ya shiga makarantar Firamare a 1979 sannan ya shiga kwalejin horas da malamai ta Dogon-Daji a 1984.

Daga nan kuma ya shiga jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto inda ya karanci aikin shari’a a 1991.

Ya kammala karatun koyon aikin shari’a na shekara daya a Legas a 1992.

Yaushe Aminu Waziri Tambuwal?

Tambuwal ya fara koyon harkokin majalisa daga 1999 zuwa 2000 lokacin da yake aiki a matsayin mataimaki kan harkokin majalisa ga Sanata Abdullahi Wali, wanda a lokacin yake rike da mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.

A shekarar 2003, ya nemi kujerar wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal a Sokoto. Aka kuma zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai karkashin jam’iyyar ANPP.
Ƴan watanni gabanin zaben gwamna a shekarar 2007, Tambuwal ya koma jam’iyyar PDP tare da tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko.

Aminu Waziri Tambuwal ya rike mukamai a majalisar wakilai. A shekarar 2005, ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai har zuwa lokacin da ya koma jam’iyyar PDP.

Bayan an sake zabarsa a shekarar 2007, an kuma sake zabarsa a matsayin mataimakin shugaban bulaliyar majalisar.

Tambuwal ya kuma rike shugabancin kwamitocin majalisar da dama ciki har da kwamitin dokoki da kasuwanci da na sadarwa da kuma na shari’a.

Ya kuma kasance mamba a kwamitin wucin gadi kan yi wa kundin tsarin mulkin kasa garambawul.

Aminu Waziri Tambuwal Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

A watan Yunin shekarar 2011 Aminu Waziri Tambuwal ya zama shugaban majalisar wakilan Najeriya ta 10 a cikin wani yanayi mai sarkakiya kuma na ba-saban-ba.

Tambuwal ya karbi ragamar majalisar ne daga hannun tsohon shugaban majalisar Dimeji Bankole.

Sakamakon rashin jituwa tsakanin majalisar ta wakilai da bangaren zartaswa, fadar gwamnati ta yi yunkurin ganin ta dasa shugabannnin majalisa da za su saurare ta.

To amma bisa rashin sa’a sai aka samu ‘yan majalisar sun yi wa bangaren zartarwar kwanta-kwanta, inda suka zabi mutumin da ba shi bangaren na zartarwar ke so ba.

A lokacin dai sai da ta kai ga jami’an tsaron ‘yan sanda sun kulle majalisar a ranar da aka sa ran zaben shugabannin majalisu, inda wasu da dama daga cikin ‘yan majalisar suka yi ta haurawa gini ta kan katanga.

Rahotanni na cewa shi kansa Aminu Tambuwal sai da ya yi shigar burtu sannan ya samu ya shige duk da cewa wasu rahotannin na cewa Tambuwal ya kwana a cikin ginin majalisar ne.

Aminu Waziri Tambuwal Da Takarar Shugabancin Najeriya

Aminu Tambuwal ya yi takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2015 inda tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya kayar da Aminu Tambuwal da sauran ƴan takarar a zaɓen fidda gwani da aka yi a birnin Fatakwal.

Amma Aminu Tambuwal ya samu kuri’u 693, wanda hakan ne ya ba shi damar samun matsayi na biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan