Auren Gimbiya Zainab Nasiru Ado Bayero: Nasihar da iyayenta su ka yi mata akan zaman aure

277

A jiya ne Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya aurar da ƴar sa Gimbiya Zainab Nasiru Ado Bayero, inda aka ɗaura auren a fadar mai martaba Sarkin na Bichi.
Kwana ɗaya ya rage a ɗaura auren Kawun Amarya kuma tsohon hakimin Kura, Alhaji Bello Ado Bayero ya yiwa amaryar wata huɗuba mai ratsa zuciya a shafinsa na facebook.
Ga cikakkiyar huɗubar:

Toh Umma kin san tarihi, lokacin kina ƙarama mahaifiyar ku (Mama) kan shirya ku da kayanku ke da ɗan uwanki Abdulkadir ku zo gidana ku zo kuyi hutu a wajena, har mu kan yi barchi da ku a gado tare da ku saboda da ƙauna a matsayin ƴaƴanmu, Alhamdulilah yau ga shi kin yi karatu daga digiri na ɗaya zuwa na biyu (Masters), bayan karatun addinin Islama da tarbiya irin ta gidanmu mai kyau da kika samu a wajenmu, da halinki na son ƴan uwa da danginki da kawunanki da girmamawa da labduka, masha Allah tabarakallah”

Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero tare da Gimbiya Zainab Nasiru Ado Bayero

“Dama ba muyi mamaki ba sunan wadda aka samiki wato uwa garemu ni da Mai Martaba Sarkin Bichi da Mallam Shehu da Mallam Zubairu, Uwar Soron Sarkin Kano Maje Juma’a, wadda ta rainemu muka tashi gurinta tun muna ƙanana har mu ka kai wannan lokaci, Allah ya ji ƙanta, don haka ne muke fatan a gidan mijinki za ki samu albarka da zaman lafiya da kowa, da kyakkawar makoma mai kyau da inganci, da hali na girmamawa da cikakkiyar tarbiya, madallah, Allah yayi miki albarka”

Wani zai yiwa Manzo Sallallahu Allaihissalam Sujuda nan da nan ya tsawatar masa, ya ce ai da akwai wadanda Allah zai sa a yiwa sujuda toh mace ce za a sa ta ringa yiwa mijinta sujuda! Subuhanallahi, muna yiwa ƴaƴanmu fatan za su bi mazajansu na aure kuma su yi musu biyayya domin aljannar su na ƙarƙashin ƙafafuwan Mazajensu. To Ummar mu, Allah ya ba ki zaman lafiya, Allah ya sanya alheri ya kuma kareki daga duk abin ki da gamawa lafiya amin”

Ɗaurin auren dai ya samu halarcin fitattun mutane da ƴan siyasa da kuma ƴan kasuwa.

Gimbiya Zainab Nasiru Ado Bayero
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan