Mai yiwuwa a sake garƙame ƴan Najeriya saboda karuwar masu Korona

256

Gwamnatin tarayya tace ba ta da wani zabin da ya wuce sake kakabawa al’ummar kasar nan dokar kulle, muddin aka cigaba da samun karuwar adadin mutanen da suke kamuwa da cutar Coronavirus, kamar yadda aka gani cikin makon da ya kare.

Yayin ganawa da manema labarai a Abuja, shugaban gudanarwar kwamitin yakar annobar ta Korona na kasa Dr Sani Aliyu yace muddin ‘yan Najeriya basa son a sake killace su, ya zama dole su kiyaye sharuddan da kwararru suka gindaya na dakile yaduwar cutar.

Kwanaki 3 a jere cikin makon da ya kare hukumomin lafiya a Najeriya suka bayyana gano adadi mai yawa na karin masu kamuwa da cutar coronavirus a rana guda fiye da ko yaushe, inda a ranar Laraba kadai 6 ga watan Janairu, cibiyar dakile yaduwar cutukan kasar NCDC ta sanar da gano karin mutane dubu 1 da 664 da suka kamu cikin sa’o’i 24.

A ranar Litinin dai mutane dubu 1 da 204 aka gano sun kamu, yayin da a Talata aka samu karin mutane dubu 1 da 354 cikin kwana guda a fadin kasar, Inda Legas, Abuja da Filato ke kan gaba wajen yawan masu cutar.

A baya bayan nan ne dai, ministan yada labaran Najeriya Lai Muhd ya ce gwamnatin kasar na ba ta da shirin sake yiwa jama’a kulle domin dakile cutar da ta sake barkewa karo na biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan