Sharhi: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga ‘Ƴan Matan’ da ba su yi aure ba

  175

  Rashin mijin aure babban ƙalubale ne da ke cin sharafinsa a duniyar ƴan mata har da zawarawa a wannan lokaci, da yawan mata sun sami kansu cikin damuwa bisa rashin mazajen aure.

  Iyaye kan tsangwami ƴaƴansu mata bisa rashin fitowa da mijin aure, akan sami gulmace-gulmace da cece-kuce daga ƴan uwa, dangi da ƙawaye, wanda kan ƙara jefa yarinya cikin Ƙuƙumi har ta yanke shawarar auren wanda ya shirya aurenta ko da kuwa bai cancanta ba wanda hakan babban kuskure ne.

  Akwai matan da rayuwa ke hukunta su bisa wasu kura-kurai da suka sabbabawa kansu. Wasu matan tun a farkon budurcinsu suke samun samari masu nagarta da sana’a wadanda suka cancanta a rayu da juna, sai buri ko ruwan ido ya hana su aure. Haka masu Mota za su yi ta sallama da su suna ɓata musu lokaci a ƙarshe dai sai ku ga sun rinjayi shekarun budurcinsu har a daina yayinsu, wanda a ƙarshe waɗannan ƴan mata a wayi gari suna neman mijin aure ido rufe duk tsufansa da rashin cancantarsa.

  Akwai matan da ƙaddara kan taka rawar gani a rayuwarsu ta hanyar rashin gam-da – katar da mijin aure nagartacce wanda jiyansu tayi muradinsa kuma gobensu za ta yi alfahri da shi, irin waɗannan mata bai kamata a tsangwame su ba matuƙar sun kama mutuncin kansu.

  An sami da yawansu wadanda tsangwamar iyaye ko cece-kucen ƴan uwa da ƙawaye ta haifar musu da riskar juma’arsu tun a ranar talatarsu su girbi shukar da ba ta su ba ta hanyar auren wanda bai cancanta ba daga baya a zo ayi hannun riga iyayen Yarinya su dinga kukan an cuci yarinyarsu ko an wulaƙanta ta, bayan sune silar faruwar hakan.

  Ƴar uwa a shawarce, ko shekararki nawa a gaban iyayenki ka da ki bari rashin mijin aure ko tsangwamar iyaye ta sa ki auren wanda ra’ayinsa ya saɓa da nagarta, ki kama kanki ki yi karatu ki kuma tashi ki nemi na kanki, ki toshe kunnuwanki daga maganganunsu na iskantar da ke, duk jimawar namiji ba aure ba a jifansa da iskanci ba tare da hujja ba, ki yawaita addu’a matuƙar kin saka Allah a ranki Allah zai ba ki miji nagari abun alfahri.

  Na san raɗaɗin da ke cikin rayuwar Zawarci ya zarce na rashin miji. Rabuwar aure lamari ne mara daɗi musamman a ce an sami ƴaƴa tsakani. Ba muna bayan mace ta ki yin aure ba ne, auren nagari wanda ya cancanta muke goyon baya wanda addini da lafiyayyen hankali ma sun mara mana baya.

  Duk wanda ya sami kansa a duniya ya sani dole yayi abota da ƙalubale. Ita kanta rayuwar aure rayuwa ce mai ƙunshe da ƙalubale, amma muddin kika sami Miji mai addini, nagarta da sana’a wanda zai mutunta ki ya ba ki hakkinki to ki aure shi kuma ki yi haƙurin zaman aure da shi.

  Allah ya baiwa ƴan matan da suke neman aure mazaje nagari.


  Indabawa Aliyu Imam, mai yin sharhi ne akan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Kano – Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan