Zan Tabbatar Tarihin Gidan Mahaifin Kwankwaso Bai Gushe Ba— Ganduje

330

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa don ganin tarihin gidan marigayi Makaman Ƙaraye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso bai gushe ba.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne ranar Asabar a ƙauyen Kwankwaso, a yayin ta’aziyyar marigayi Musa Saleh Kwankwaso, wanda yake mahaifi ne ga tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamna Ganduje ya ce ƙaunar da take tsakaninsa da marigayin ba za ta misaltu ba, a don haka ba zai bar tarihin gidan nasa ya salwanta ba, kamar yadda jaridar Intanet mai bada labaran Kano zalla, Kano Focus ta rawaito.

Ya ƙara da cewa rashin Makaman na Ƙaraye ya bar babban giɓi ba kawai a jihar Kano, har ma da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ji ƙan marigayin, Ya ba wa iyalansa haƙuri.

Turawa Abokai

2 Sako

  1. Kwankwaso yakarbi hakimancin Dan NASA ne yanzu tunda babu baba yau Kuma bazai Hana shi yin harkallansa ba a duniya

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan