Ziya’ul Haqq: Mutumin Da Ya Ɗora Fakistan Kan Tafarkin Muslunci

309

A ranar 17 ga Agusta, 1988 ne Shugaban Fakistan, Janar Muhammad Ziyaul Haqq ya rasu sakamakon haɗarin jirgin saman da ya afku a ƙasar.

Janar Ziyaul Haqq ya shugabanci Fakistan tsawon shekaru tara, abin da yasa ya sa ya zama shugaban ƙasar mafi daɗewa kuma mafi tasiri a tarihin ƙasar, musamman ayyukansa na gina sabuwar Fakistan bisa tsarin Musulunci.

An haifi Janar Ziyaul Haqq a ƙauyen Jalandhar cikin jihar Punjab ta tsohuwar Indiya a ranar 2 ga Agusta, 1924.

Bayan ya yi digirinsa a Kwalejin St. Stephens, ya shiga sojan Turawan Indiya a shekarar 1943, ya yi aikin soja a gurare masu yawa har ya kai matsayin janar a shekarar 1976, wanda Firaministan Ƙasar, Zulfikar Ali Bhutto ya naɗa shi Shugaban Sojojin Ƙasar, duk da yake akwai wasu manya a gabansa, (Mujallar Herald, Yuli, 1992).

An ce akwai sojoji kimanin 7,000 dake gaba da Ziyaul Haqq, wannan ce ta sa a ranar da Firaministan yake bikin sanya masa tauroro huɗu (Muƙamin Janar), kuma shugaban sojojin ƙasar, yake faɗa masa cewa: “Ya kai shugabana! Ba shakka a yau ina cike da farin ciki na wannan muƙami da ka ba ni na shugaban sojoji, ba ni kaɗai ba har waɗanda za su biyo bayana za su ci gaba da tunawa da kai bisa wannan girmamawa da ka yi mini, wannan wata alfarma ce da ba zan taɓa mantawa da ita ba har abada”.

An ce Zulfikar Bhuto ya yi haka ne saboda riƙon addini da ya gani a wajen Ziyaul Haqq da kuma tunanin makomar siyasar ƙasar. (Duba littafin Pakistan: Between Mosque And Military; From Islamic Republic To Islamic State. Hussaini Haqqani (2005), United State Carnegie Endowment For International Peace. Shafi Na (395).

Tun daga shekarar 1976, rigingmun siyasa suka dabaibaye ƙasar, abinda ya sa Bhutto sanya dokar ta ɓaci ta Martial Law a wasu manyan jihohi da suka haɗa da; Karachi, Lahore, da Hyderabad. (Duba Littafin Prospects For Peace In South Asia. Rafiq Dossani (2005). Standard University, Press. Shafi Na (46-50).

Wannan da wasu dalilai suka sa a shekarar 1978, Janar Ziyaul Haqq ya yi juyin mulkin da ya kau da gwamnatin mai gidansa, Zulfikar Ali Bhutto, tare da garƙame shi a kurkuku.

A lokacin da ya zama Shugaban Ƙasar, duk da rigingimu na gida da na waje da ya yi ta fama da su, Janar Ziyaul Haqq ya yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen ɗora ƙasar bisa tsarin Shari’ar Musulunci, ya kafa Majalisar Shura wadda ta maye gurbin Majalisar Ƙasa, inda ya sa manyan malamai da masana da ƙwararru a kowane ɓangare, cikinta.

A cikin waɗanda aka sanya a Majalisar Shurar har da Dakta Asad, wanda ya yi ƙoƙarin ƙara yawan man fetur da ƙasar ke haƙowa, da ƙwararren malamin Fiƙihun nan, Sharfuddeen Perzada da masanin Tattalin Arziƙi, Mahbubul Haq da sauransu.

Haka kuma, Muhammad Ziyaul Haqq, a ƙoƙarinsa na tabbatar da Shariar Musulunci, duk da matsalolin da ya yi ta fuskanta, ya amince da sauya hukunce-hukuncen Musulunci a tsarin mulkin ƙasar wanda ake kira da ‘Islamic Bench’, wanda ya haɗar da; rajamu, yin bulala ga mazinaci da batun biyan diyya, da sauran hukunce-hukunce na Shariar Musulunci.

Haka kuma, a tsarin tattalin arziƙi na ƙasar, gwamnatin Ziyaul Haqq ta yi ƙoqarin Musuluntar da tsarin kasuwanci da bankuna, inda aka tsarkake bankunan ƙasar har 7,000 daga tsarin riba (interest) da kuma ɗora su kan tsarin Zakka da sauran alamuran addinin Musulunci.

Wani abu da ake tunawa da Ziyaul Haqq wajen taimakon addinin Musulunci a lokacin mulkinsa shi ne yadda ya taimaka wajen bunƙasa Ilimin Addinin Musulunci a ƙasar, musamman buɗe makarantun addini, da ƙara yawansu daga 893 zuwa 2,801, inda ya ba su kyakyawar kulawa da ɗaukar nauyinsu da ba a taɓa samun irinsa ba.

A lokacin yaƙin mujahidan Afghanistan da Tarayyar Soviet ta mamaye, Ziyaul Haqq ya goyi bayan mujahidan tare da taimaka musu har dai dole Soviet ta fice daga Fakistan a shekarar 1989.

A ranar 19 ga Disamba, 1984, Janar Ziyaul Haqq ya gabatar da taron gyara tsarin mulki (referendum), inda kaso 95 cikin ɗari na alummar ƙasar suka amince da zarcewarsa a matsayin Shugaban Ƙasa.

A shekarar 1985 aka tabbatar da Kundin Tsarin mulkin Ƙasar, kuma aka zaɓe Janar Ziya’ul Haqq a matsayin zaɓaɓɓen Ƙasa.

A lokacin da ya zama Shugaban Ƙasa, Ziyaul Haqq ya naɗa Muhammad Khan Jinejo a matsayin Firaminsta, wanda ya yiƙqarfi har ana ganin ya fi Shugaban Ƙasar tasiri ta hanyar gyara Tsarin Mulki Na Takwas da aka yi ba tare da sanin Shugaba Ziyaul Haqq ba.

Wannan ta sanya shugaba Ziyaul Haq ya tuɓe tare da korar Junejo daga Firaminista bayan da ya amince da sanya hannu a kan yarjejeniyar Geneva Accord wadda take sasanta rikici tsakanin Falasɗinawa da Israila, ba tare da amincewar Shugaba Ziyaul Haqq ba.

Wannan ta sa ya kori Junejo, kuma ya shirya yin zaɓe a Nuwamba, 1988, amma kwatsam a ranar 7 ga Agusta, 1988, sai jirgin sama ya faɗi da Shugaba Ziyaul Haqq da wasu manyan jamian gwamnatinsa, ciki har da Shugaban Sojojin Ƙasar, Janar Akhtar Abdurrahman da Ambassadan Amurka, Arnold Raphael.

Bayan bincike da aka yi ta yi an fitar da rahotanni mabambanta game da sanadiyyar rasuwar Shugaba Ziyaul Haqq, kamar yadda wani ɗan jaridar ‘New York Times,’ Barbara Crossette ya rubuta cewa: Duk wata rigimar kisan kai da ta faru a ƙarni na 20, ba wadda Amurka ke da hannu dumu-dumu fiye da haɗarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar rasuwar Shugaban Fakistan Janar Muhammad Ziyaul Haqq ba”.

Allah ya ji ƙan Janar Muhammad Ziyaul Haqq, Ya saka masa bisa ayyukan da ya yi wa addinin Musulunci. Allah Ya gyara shugabannin Musulmi, Ya ba su ƙarfin halin hidimta wa Addinin Allah. Allah Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, Ya sa mu gama lafiya.

Aliyu Ibrabim Sani Mainagge malami ne, marubuci kuma manazarci.
Ya rubuto daga Kano.
Za a iya samun sa a kan lambar waya: 08068985599, ko adireshin imel: alibabapress2021@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan