Tsakanin Miji da Mata wa ya kamata ya godewa wani?

  178

  Godiya muhimmiyar al’amari ce a zamantakewar yau da kullum. Mutane kan yita fatan tulin ni’ima da burin duk abin da suka nema su samu wasu ma cikin gaggawa amma kash yayin da suka samu sai su manta silar nan da ta sada su da burin nasu.

  Tsakanin miji da mata duk kowannensu ana bukatar su kasance masu godiya ga junansu yayin da duk wani abu na alheri ya gitta ita kuwa wannan godiyar ba fa iya a fatar daki ta tsaya ba alamomin godiya suna da yawa.

  Yayin da duk namiji ya ba ki kyauta komai komai kankantarta ki amsa ki ce maddallah kin gode kuma cikin yabwa da sakin fuska yana kara sa shakuwa sannan kin ba shi kwarin gwiwa ne don ya ke yi miki kyauta ba kasala.

  In namiji ya kawo kayan abinci gida duk da hakkinsa ne ci a sha wajibinki ne ki gode masa saboda sai ki kalli wasu gidajen makusantanki ki ga su ba su samu kamar wannan ba watakil ma nakin bai kai su samu ba amma shi yana da tausayin kawowa gida.

  Hatta wani aiki in ya yi a gida kamar gyaran kofa ko da kofar dakinsa ce ko aka kira mai ruwa ko da shi ne ya fi ki amfaranar ruwan wajibi ne ki gode masa.

  A hidima irin ta sallah yana da kyau uwar gida take godewa ki tuna namiji yana da nauye-nauye da dama a kansa ba kamar mace ba don haka yayin da ya kawo ya ba ki ki karba ki gode. Godiya na sa wa a kara yi ma kyauta ko ba a yi niyya ba.

  Akwai hanyoyin nuna godiya da dama daga cikinsu akwai:

  Godiya Ta Fatar Baki:

  Godiya ta fatar baki ita ce irin kalaman da za ki furta don yin godiya da addu’a na neman Allah ya kara budawa.

  Godiya Da Gabobi:

  Ba wai iya fatar baki ne kadai a ke furta godiya ba; akwai amfani da gabobi wanda zai wakilci godiya kamar:-

  Runguma: A na nuna godiya ta hanyar runguma don nuna jin dadi da godiya

  Sumbata: Sumbata ko kiss lokacin da aka yi miki abin alheri shi ma wata hanya ce ta nuna jin dadi da godiya da nuna shakuwa tsakanin iyali.

  Murmushi: Murmushi yana wakiltar godiya da nuna farin ciki a wasu lokutan inda duk lokacin da aka yi miki alheri ki ka saki fuskarki da lallausan murmushi.

  Aikin Alheri: Hanyar godiya akwai ayyukan alheri wato saka alheri da alheri. Lokacin da namiji ya yi miki kyauta ko ya sauke wani nauyi to abu muhimmi shi ne ki rubanya ayyukanki na alheri a gare shi. Misali in kayan abinci ne ki kyautata masa ya ga sauyi ki yi masa wani abu na musamman na ci ko ki yi wata kwalliya fiye da wadda ki ke yi in za ki fita biki.

  Alheri: Yi wa iyayen mijinki ko wani makusantansa in ba shi da mahaifa wani alheri daidai karfinki shi ma yaba kyauta ne.

  Ba mace kadai ce ake so ta yi godiya bah ar da namiji don rashin yabawa mata na kawo cikas a cikin sha’anin aure don kuwa mace tana bukatar yabawa da godiya.

  Akwai abubuwa da dama da ya kamata maza su godewa matansu duk da ayyukan da suka yi zai iya zama yi wa kai ne to amma to da ba ta yi a kuma cutuwarka ce.

  Misali:-

  Idan mace ta yi ma girki ko ta fitar da kai kunya a idon abokai ko ‘yan’uwa ko ta kankaro maka mutunci a inda in ta kau da kai girmanka ne zai zube ko ta tarbiyyantar da yaranka ko yaranka suka yi wani abun kirki a makaranta kamar kokari ko wani ladabi ya zama wajibi ka godewa matarka wadda ita ce sila don da babu kulawarta duk wannan nasarar da jin dadin da ka yi na abin kirkin da ‘ya’yanka suka yi matarka it ace sila don haka ya kamata ka gode mata.

  Hatta bayan gabatar da sunnar aure yana da kyau ka yi wa matarka godiya kamar ita ma ya kamata ta yaba maka. Ya kamata ka gode mata ta yadda ta zama ta kare ka da jefa sha’awarka a haramun.

  Yayin da ka tarar an gyara gida an share ko’ina tsaf-tsaf ya na kamshi, to ya kamata ka yi wa uwargida godiya don ka gani ka ji dadi.

  Kada ka manta yawan yi wa mai dakinka godiya yana kara mata kwarin gwiwa wajen zage dantse don ci gaba da kyautatawa. Hanyoyin da mace ke bi, don yi wa namiji godiya sune dai hanyoyin da namijin shi ma ya bi don ya yi mata godiya.

  Don haka godiya tsakanin mace da namiji a zamantakewar aure raba dai-dai aka yi kowa ya na bukatar godiyar kowa.

  Bilkisu Yusuf Ali, Malama Ce A Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina, Ta Rubuto Daga Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan