Ya Kamata Atiku Ya Daina Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa— APC

150

Jam’iyyar All Progressives Congress APC, mai mulki a Najeriya, ta yi kira ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaɓen 2019, Atiku Abubakar da ya yi watsi da takarar Shugaban Ƙasa a 2023, tana mai cewa PDP ba za ta iya dawo wa Aso Villa ba a 2023.

Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa a Arewa Maso Gabashin Najeriya, FarfesaTahir Mamman ne ya yi wannan kira ranar Asabar a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a yayin da ya kira taron manema labarai don wayar da kan ‘yan jam’iyyar game da aikin yi wa sabbin ‘yan jam’iyya rijista da kuma aikin tabbatar da sahihan ‘yan jam’iyyar za a yi a nan gaba.

Farfesa Mamman, wanda ya ce APC tana yunƙurin samun mutane fiye da miliyan biyu a Adamawa a matsayin ‘ya’yanta, ya lura da cewa yana da muhimmanci a matsayinsu ‘yan asalin jihar su sanar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar kada ya sake ya yi asara a siyasance tun da ba zai iya cin zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 ba.

Ya kuma ce Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, zai sha kaye a zaɓen 2023.

“Idan Allah Ya yadda, a 2023 za a yi APC SAK a dukkan matakai, matakin ƙasa, na jihohi zuwa ƙananan hukumomi. Da irin wannan sabon ƙarfi namu, duk ‘yan takararmu da suka lashe zaɓukan fitar da gwanaye za su ci zaɓukan gaba”, in ji shi.

Sai dai a wani martani da ya mayar cikin gaggawa, Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Fintiri, Humawashi Wonosikou, ya ce: “APC tana mafarki ne yayin da take a tsaye”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan