Za Mu Ci Gaba Da Ɗaukar Shirin Labarina Ranar 15 Ga Janairu— Aminu Saira

160

Aminu Saira, mai bada umarni a fitaccen shirin nan mai dogon zango, Labarina, ya bayyana cewa za su ci gaba da ɗaukar shirin Zango na 3 da na 5 ranar 15 ga Janairu, 2021.

Saira ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi da daddare.

“In sha Allah, Juma’a mai zuwa 15/1/2021 za mu ci gaba da ɗaukar shirin #LABARINA Series Zango na 3 da na 4. (season 3 & 4) Da zarar aikin ya fara nisa za mu sanar da lokacin da za a ci gaba da haska shi. Allah muna neman taimakonKa. Allah Ka iya mana da iyawarKa”, in ji Saira.

Labarina shiri ne mai dogon zango da ya samu karɓuwa a tsakanin mutane, kuma an fara nuna shi ne ranar 5 ga Yuli, 2020.

An nuna shiri na ƙarshe ne a Zango na 2 ranar Litinin, 28 ga Disamba, 2020.

Tun lokacin ma’abota kallon shirin ke ta son jin yaushe za a ci gaba da nuna shirin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan