Ƴan bindiga sun ƙwace ƴancin da walwalar ƴan Najeriya – Wole Soyinka

4

Shararren marubucin nan, mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka ya caccaki gwamnatin tarayya a game da yadda rashin tsaro ya yi kanta a fadin kasar, yana mai cewa kungiyoyin ‘yan bindiga sun dakile wa kasar yancinta.

Ya ce akwai bukatar shugaba Muhammadu Buhari ya zage dantsi wajen taka wa Boko Haram da sauran masu aikata muggan laifuka da ke barazana ga tsaron Najeriya birki.

A wata ganawa da aka yi da shi a wata tashar talabijin mai zaman kanta, Soyinka ya ce matsalar tsaro a kasar ta girmama, kuma ba za a samu mafita ta wajen zama kurum a fadar Aso Rock ba.

Soyinka ya ce yanzu matsalar ta tsaro ta shafe kowa da kowa, har ma da mafi kankanta a cikin ‘yan kasa, duba da cewa shine masu satar mutane don karbar kudin fansa suke hari.

Baya ga ayyukan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, satar mutane da ‘yan bindiga ke yi a arewa maso yamma ya zama ruwan dare.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan