Adabi: An buɗe gasar rubutun Hausa ta marigayi Abubakar Imam

180

Gidauniyar Sana’a da Ilimi ta sanar da buɗe gasar rubutun ƙagaggun labarai na Hausa, domin tunawa da marigayi Alhaji Abubakar Imam.

Shafin Labarai24 ya samu sanarwar buɗe gasar ne daga shafin shugabar gidauniyar ta Sana’a da Ilimi, Amina Ado, na manhajar Linked.

Sanarwar ta ƙara da cewa a shekarar 2019 ne gidauniyar ta Sana’a da Ilimi ta ɓullo da wannan gasa, sai dai abin takaici har wa’adin rufe gasar ya yi ba a samu ko mutum ɗaya da ya jarraba ba.

Tun da farko dai an ƙirƙiro gasar ne da nufin ƙarfafa gwiwar marubuta ƙagaggun labarai a harshen Hausa. Haka kuma ana sa ran duk wanda ya zo na ɗaya zai karɓi kyautar tsabar kuɗi Naira Dubu Ɗari Biyar (500,000).

A ƙarshe za a rufe karɓar labaran ne a ranar 31 ga watan Maris din shekarar 2021.

Waye Ya Cancanci Ya Shiga Gasar?


Kowa zai iya shiga Gasar, sai dai sharaɗin shi ne;

1 – Rubutaccen ƙagaggen labarai wanda aka wallafa shi a shekarar 2019 ko 2020.

2 – Za miƙa kwafin littatafai guda uku da aka wallafa kafin ranar 31 ga watan Maris, kuma an so a tura kwafin littattafan ta adireshin imail kamar haka : info@sanaadailmi.com.

4 – Haka kuma ana buƙatar a haɗo da lambar shaida kamar Katin Ɗan Ƙasa ko makamancin haka na mawallafin.

Wanene Alhaji Abubakar Imam?

Marigayi Alhaji Abubakar Imam

An haifi Abubakar Imam a garin Kagara na jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya a shekara ta 1911. Marigayin ya yi fice wajen rubutun kagaggun labarai na Hausa.

Abubakar Imam ya yi karatunsa na boko a jihar Katsina a makarantar nan ta Middle School da ke Katsina da kuma Katsina Training College sannan ya yi karatu a tsangayar ilimi ta jami’ar London da ke Burtaniya.

Bayan da ya kammala karatunsa, ya yi koyarwa a Katsina sannan kuma ya yi aiki matsayin edita na jaridar nan ta Gaskiya Ta Fi Kwabo kana ya tallafawa masarautar Katsina ta wancan lokacin karkashin shugabancin Alhaji Muhammadu Dikko inda ya ke fassara rubuce-rubuce daga Larabaci zuwa harshe Hausa.

Alhaji Abubakar Imam ya yi fice ne lokacin da aka sanya wata gasa ta rubutun kagaggun labarai a shekara ta 1933 inda wani littafi da ya rubuta mai suna Ruwan Bagaja ya yi nasara a cikin litattafan da aka rubuta. To baya ga wannan littafi, marigayin ya kuma rubuta wasu litattafan da dama da suka hada da Magana Jari da Ikon Allah da Tarihin Annabi (S.A:W:S) da Tarihin Musulunci da Auren Zobe da makamantansu.

Marigayi Abubakar Imam na daga cikin marubutan da dalibai a matakai daban-daban ke yin nazari kan littafan da suka rubuta da ma nazari kan rayuwarsu. Allah ya yi masa rasuwa cikin shekara ta 1981 ya kuma bar yara goma sha hudu, maza bakwai da kuma mata bakwai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan