Duk Wanda Ya Saki Mace A Fim Matarsa Ta Gida Ta Saku— Dakta Bashir

660

Babban Limanin Masallacin Juma’a na Alfurƙan dake jihar Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar ya ce duk wanda ya saki mace a cikin shirin fim to hakan daidai yake da sakin matarsa ta gida.

Daktan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo, inda aka gan shi yana bayani game da yadda al’umma ke wasa da al’amarin saki.

A cewar Dakta Umar, duk wani ɗan wasa da ya furta wa matarsa ta fim saki, to ba bu shakka ya saki matarsa ta gida, kuma babu aure a tsakaninsu, kamar yadda jaridar Intanet mai bada labaran Kano zalla Kano Focus ta rawaito.

“Ko da wasa idan ka zo aka daura maka aure a fim, mutum ya ce ya saki matansa kuma yana da mata, kuma ya faɗa ya ce ai matan nawa duk na sake su, wai yana nufin matansa na wasan Hausa, to na gasken sun tafi.

“Ba a wasa da sha’anin saki ko kuma aure. Ka zo a cikin wasan Hausa a ce an ɗaura maka aure, san nan ka ce kuma wannan ba aure ba ne? Kuma an ɗaura aure an cika sharaɗan aure, to aure ya ɗauru”, in ji Dakta Umar.

Ya ƙara da cewa ce yawancin waɗanda ke fitowa a matsayin kafirai a cikin shirin finafinai su ma suna da gagarumar matsala ta rasa Musuluncin gaba ɗaya.

Turawa Abokai

8 Sako

  1. Sai malam yakawo hujoji da ayoyi da hadisai ba fadin ra’ayinsa kawaba indan kuma babu ayan rur’ani ko hadisi to wannan magana na yan barasa ne

  2. Kennan Mai mata hudu idanya fito am tsayin mini wata ya Kara aure Kennan?
    Kuma in yakai hadisin innamalamali binniyati .

  3. Toh amma ai akawai Hadith din dayace Allah da zuciya yake duba ina ganin kamar mgnr k taci karu d wannan hadisin Allah ya gafarta mana ameen

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan