Hattara: Akwai wani shiri na tayar da rikicin addini a jihohin Kano da Sokoto – DSS

132

Hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasa DSS ta ce ta bankaɗo wani shiri na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a wasu jihohin ƙasar nan.

Sanarwar da kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar a yau Litinin ta yi gargadi ga al’ummar ƙasar nan kan abin da ta ce wasu na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a sassan ƙasar nan.

Kuma sanarwar ta ambaci jihohi da suka ƙunshi Sokoto da Kano da Kaduna da Filato da Rivers da Oyo da Legas da ta ce ana shirin tayar da rikicin addini. “Wani ɓangare na shirin shi ne haifar da rikice-rikice tsakanin addinai tare da kai hari wasu wuraren ibada da shugabannin addinai da wasu manyan mutane kuma wasu muhimman wurare,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta yi gargaɗi ga ƴan Najeriya su yi hankali kuma su guje wa duk wasu daɓiu da nufin tunzura su ko tayar da rikici tsakanin junansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan