Mustapha Bala Getso ya koma jam’iyyar PDP ɓangaren gidan Marigayi Abubakar Rimi

254

Tsohon ɗan takarar gwamnan a jam’iyyar NPM a zaɓen shekarar 2015, Mustapha Bala Getso ya sauya sheƙa daga jam’iyyar da ya yi takara ta NPM zuwa jam’iyyar PDP ɓangaren gidan marigayi Muhammad Abubakar Rimi.

Tun da farko kakakin ƴan jam’iyyar PDP masu ra’ayin Muhammad Abubakar Rimi, Kwamared Aminu Sa’ad Beli ne ya bayyana hakan a shafinsa na facebook.

Idan za a iya tunawa dai Mustapha Bala Getso dai ya yi takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NPM, inda ya bayyana cewa inda ya zama gwamnan Kano zai kawo tsarin iyali a yunkurinsa na magance matsalar almajiranci. Ya ce zai wayar da kan iyaye su daina haihuwar ‘ya’ya rakwacam suna tura su bara.yana mai shan alwashin bunkasa kananan sana’o’i irinsu kafinta da walda da gini.

An yi taron karɓar Mustapha Bala Getso da tawagarsa zuwa jam’iyyar PDP a buɗaɗɗen filin taro na gidauniyar Kano da ke kan titin zuwa jami’ar Bayero, inda ya samu halarcin fitattun ƴan siyasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan