Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Karɓi Riga-kafin COVID-19 Da Zarar An Samu— Sanusi

137

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi gaggawar karɓar riga-kafin COVID-19 da zarar gwamnati ta samar da shi.

Tsohon Sarkin ya yi wannan kira ne a yayin wani taron wayar da kai kan rigakafin da likitoci ‘yan Najeriya mazaunan kasar waje suka gudanar ranar Lahadi ta allon sadarwa na ga-ni-ga-ka, wato Zoom, kamar yadda jaridar Intanet mai bada labaran Kano zalla, Kano Focus ta rawaito.

A ta bakinsa, yana da matuƙar amfani shugabanni su ilimantar da al’umma muhimmnacin da yin riga-kafin ke da shi.

Ya ce matukar aka wayar da kan jama’a kan muhimmnacin riga-kafin, to babu shakka jama’a za su daina yin shakku game da sahihancinta.

“Ina kira ga al’umma baki ɗaya da a karɓi wannan riga-kafin idan ya zo.

“Kuma ina kira ga shugabanni da su mayar da hankali wajen ilimantar da al’umma da kuma jagoranci.

“Shugaba ya fito shi da kansa ya karɓa a gani, shi ne zai sa al’umma su samu kwanciyar hankali su karɓa.

“Su shugabanni su karɓa, malamai su karɓa, yara su karɓa, mahaifansu su karɓa.

“Mutane su sani, sun san cewa ba za su ba wa al’umma abin da su suka guje shi ba”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan