Mu zamu lashe zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano – PDP

133

Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, ɓangaren gidan Ambasada Aminu Bashir Wali, da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya sha alwashin samun nasara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano da za’a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Da ya ke gabatar da jawabi a wajen bikin rabawa ƴan takarar jam’iyyar PDP tuta da ya gudana a ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Mahmina Baƙo Lamido ya ce ƴan Najeriya sun gaji da mulkin kama karya da jam’iyyar APC ta ke yiwa ƴan ƙasar nan, saboda haka ƴan takarar jam’iyyar PDP, su sha kuruminsu domin su ne za su lashe zaɓen da za’a gudanar na ƙananan hukumomi a jihar Kano.

A nasa Jawabinsa Alhaji Yahaya Bagobiri, wanda shi ne ya wakilci Jagororin jam’iyyar ta PDP Ambassada Aminu Bashir Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya yi kira ga ɗaukacin ƴaƴan jam’iyyar da su tabbatar sun zaɓi PDP, tare da jajircewa wajen ganin sun kafa sun tsare sun kuma tabbatar da zaɓen da su ka yi.

A ƙarshen taron an rabawa ɗaukacin ƴan takarkarin jam’iyyar da mataimakansu tuta da suka fito daga ƙananan hukumomi 13 na shiyyar arewacin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan