Home / Labarai / Ƙasar Amurka ta zartas da hukuncin kisa na farko a cikin shekaru 68

Ƙasar Amurka ta zartas da hukuncin kisa na farko a cikin shekaru 68

Kotun kolin ƙasar Amurka ta bayar da umarnin zartas da hukuncin kisa kan Lisa Montgomery duk da bayanan da ke bayyana shakku kan cikakkiyar lafiyar kwakwalwarta, hukuncin da zai zama irinsa na farko da kasar ta yanke tun bayan 1953.

Kotun wadda ke kokarin bin umarnin Donald Trump wajen tabbatar da dawo da hukuncin kisa gabanin karewar wa’adinsa nan da kwanaki 7 masu zuwa, ta umarci gidan yarin da ke tsare da Montgomery mai shekaru 52 da ya zartas mata da hukuncin ta hanyar yi mata allurar guba da za ta saukaka mutuwa.

Lisa Montgomery, wadda kotu ta samu da laifin kisan wata mata mai juna biyu tare da sace dan cikinta a shekarar 2004, lauyanta Kelley Henry ya bayyana hukuncin a matsayin mai cike da rashin adalci.

Tun a shekarar 2007 ne kotu ta samu Montgomery da laifin kisa tare da satar yaro inda aka yanke mata hukuncin kisa amma kuma lauyoyin da ke kare ta suka daukaka kara.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Micheal Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya cika shekaru 85 da haihuwa

A yau Litinin 10 ga watan Mayun shekarar 2021 mutumin nan da ya zama tutar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *