Ba Mu Ɗaga Ranar Komawa Makarantu Ba— Gwamnatin Tarayya

366

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi watsi da rahotannin da suke zagayawa cewa ta daga ranar komawa makarantu ta 18 ga Janairu, 2021, sakamakon zagayowar COVID-19 a karo na biyu.

Daraktan Watsa Labarai da Huɗɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Ben Bem Goong, ya shaida wa jaridar LEADERSHIP ranar Talata cewa za a duba ranar komawa makarantun ne kawai a wuraren da ake ci gaba da samun ƙaruwar masu kamuwa da COVID-19.

“Gwamnatin Tarayya ba ta ɗaga ranar komawa makarantu ta 18 ga Janairu ba. Ministan ya ce kawai za a duba ranar 18 ga Janairun ne daidai da raguwa ko ƙaruwar COVID-19.

“Saboda haka, idan a gobe Kwamitin Yaƙi da COVID-19 ya ce mun samu waɗanda suka kamu mutum 5000 kuma ba za mu iya dawowa ba, wannan shi ne dubawar da muke magana a kai”, in ji Mista Goong.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana a wajen taron Kwamitin Yaƙi da COVID-1 na Shugaban Ƙasa cewa Gwamnatin Tarayya za ta duba ranar komawa makarantu don ɗaukar matakin ƙarshe.

An jiyo Ministan yana cewa: “Za ku yadda da ni cewa abin da yake faruwa yanzu ba mai faranta rai ba ne. Kuma tun kafin mu sanar da ranar komawa makarantun, an yadda cewa ranar ba wai wadda ba za a iya sauyawa ba ce”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan