Gwamna Ganduje ya naɗa Muhammad Sulaiman Gama mataimaki na musamman

266

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗin fitaccen ɗan jaridar nan wato Muhammad Sulaiman Gama a matsayin babban mataimaki na musamman akan harkokin yaɗa labarai ɓangaren da su ka shafi Rediyo da Talabijin Latoroni (Electronics Media).

Muhammad Sulaiman Gama fitaccen ɗan jarida ne da ya yi shuhura sosai, musamman a lokacin da ya ƙirƙiro wani shirin siyasa da aka kirawoshi da suna Kowanne Gauta, shirin da ya ke baiwa ƴan siyasa dama wajen faɗar ra’ayin bakinsu.

Ana kallon naɗin na Muhammad Sulaiman Gama zai ƙara taimakawa gwamnatin Ganduje ƙarfi a harkar kafafen yaɗa labarai, la’akari da irin gogewar Sulaiman Gama ɗin ya ke da ita.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan