Sakin Aure: Tsakanin Gaske da Gangan

279

A wannan makon ne wani bidiyon tafsirin babban malami Dr. Bashir Aliyu Umar ya karade shafukan yanar gizo game da wata fatawa da ya bayar game da sakin aure a cikin fim, cewar daidai ya ke da ka saki matarka ta sunna, abinda ya haifar da cece kuce, wanda ya sa nima zan ce wani abu. Hakika fahimtata ta yi karo da ta yayan nawa, babban malaminmu bisa dalilai da zan zayyana.

Abu na farko shine a cikin bayanin nasa akwai abubuwa guda hudu da ya kamata mu yi nazari, wato ma’anar wasa, fahimtar menene saki da kuma duba hadisin da ya kafa hujja da shi tare da wani hadisin da yayi karo da hujjar tasa. Idan mu ka kalli Kalmar “wasa” a mahangar Qur’ani Allah da kansa ya sanar da mu cewa Q44:38 “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu ba, alhali mu na masu wasa”

Hakika wannan zance gaskiya ne, Allah bai halicce mu don wargi ba domin a dalilinsa ya sanar da mu cewa Q51:56 “Ban halicci aljanu da mutane ba sai domin su bauta mini”

Shin hakan ya kawar da wasa kwata-kwata kenan a tsarin rayuwarmu? Ko kadan domin a tsarin halittu, ba ma Dan Adam ba hatta dabbobi Allah ya tsara mu a yanayi da wasa na cikin ginshikin habakar halittar gangar jiki da kwakwalwa musamman a kananan shekaru na rayuwa. Ba wani mahaluki ko dabba da a yayin tasowa na yarinta bai kasance ya na wasa ba domin hakan ke habaka sassan jiki da na kwakwalwa. Annabi ya kasance mutum mai tsananin son yara da wasa da su, saboda fahimtar tasirin wasa a rayuwar yarinta. Ba a yarinta kawai ba, hatta a cikin girma wasa na da mahimmanci wajen habaka sassan jiki da kwakwalwa da nishadantarwa, shi yasa hadisai da dama sun zo da tsarin wasanni da Allah ya halatta wadanda Annabi da kansa ya yi wasu, kamar wasannin harbin kibiya, kokawa, ninkaya, gudu da tseren doki. Zamu iya fahimta cewa wasa na da alaka biyu, wato a aikace (kamar irin wadancan wasanni da na jero) da kuma a niyyance (wadanda ke jibantar mu’amala tsakanin mutane da ya jibanci niyya).

Cewar idan dan fim a cikin shirin fim ya saki matarsa ta cikin fim, tamkar ya saki matarsa ta aure ne ya yi karo da abubuwa kamar haka: Na farko dai sharadin saki ba ya wanzuwa sai a cikin aure, domin duk gwaninta ta na iya saki ba zan iya sakin wadda ba matata ba, dole sai aure ya shiga tsakina da ke sannan zan iya sakin ki, to idan ban aure ki ba, ta yaya zan iya cewa na sake ki? Hakan ya tabbata cikin hadisin Abu Dawud da Amr ya ruwaito cewa babu saki sai da mallaka. Kamar yadda wani dalibi a zauren da Malam ke bayar da wannan fatawa ya yi wuf ya tambayi malam game da hurumin niyya a ayyukan musulunci, amma malam ya kawar da niyya da wani hadisin, to amma kafin duba hadisin da ya kawo mu duba me musulunci ya ce game da niyya. Allah da kansa ya ce Q9:105 “Kuma ka ce “ku yi aiki, sannan Allah zai ga aikinku, da manzonsa da muminai, kuma za’a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sannan ya baku labarin abinda kuka kasance kuna aikatawa”

Wato aiki ya danganta da niyya, kuma Allah shine mafi sanin niyyar mu kuma da ita zai yanke mana hukunci. Duk wanda ya taso a wannan yanki namu idan ya yi karatun musulunci ya san shahararren hadisin Nawawi cikin arba’una hadith da Umar ya ruwaito cewa “Dukkan ayyuka sai da niyya…” har karshen hadisin wanda ke nuna cewa ayyukan zahiri ba su ne a’ala ba sai abinda bawa ya kudurce a zuciyarsa kuma da alamu wannan hadisi tafsirin ayar nan ce da Allah ke cewa Q22:37 “Namominsu ba za su sami Allah ba, haka jininsu, amma takawa daga gare ku ta na samunsa”

To amma malam a bayaninsa ya kawo hadisin Abu Dawood wanda da ya ce ya kore niyya a wasu abubuwa kamar haka “Abu Huraira ya ruwaito cewa “Manzon Allah (SAW) ya ce “Abubuwa guda uku yin su da gaske ko da wasa zai tabbata: Aure, saki da kome (idan sakin bai kai uku ba” Wannan hadisi na nuna girman yadda addini ya dauki matsayin aure da saki ne, domin kamar yadda Allah ya ce bai halicci sammai da kasa don wasa ba, haka nan harkokin addini musamman ginshikai ba’a wasa da su. Hakan zai fito mana karara idan muka duba yadda tsarin, musamman saki, ya ke a wurin ubangiji domin a cikin hadisin Abu Dawud din dai ya zo cewa Muharib ya ruwaito cewa: Annabi (SAW) ya ce: Ba wani abu da Allah ya halarta kuma ya ke kinsa kamar saki” Sakamakon haka sai Allah ya kafa dokoki masu tsauri da shingaye masu ma’ana kafin yin saki da kuma tabbatar sakin.

Da farko dai sai Allah ya umarci miji, kasancewar shi ke da igiya ta farko a cikin saki da cewa Q4:34 “…kuma wadanda kuke jin tsoron bijirewarsu to ku yi musu 1. Gargadi 2. Ku kaurace musu a cikin wuraren kwanciya 3. Ku doke su”

Wadannan su ne matakan farko a saki da dole sai an bisu. Idan kuma duk wadannan hanyoyi ba su yi tasiri ba, sai Allah ya ya bayar da mataki na gaba da cewa Q4:35 “Idan kun ji tsoron sabawar tsakaninsu, to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa (su ma’auratan) Allah zai daidaita tsakaninsu”

Wannan aya na dada nuna mana cewa maganar saki ba ta tsaya ga ma’aurata kawai ba. Idan har an zo wannan mataki na sulhu a gaban magabata, matukar ma’auratan na da dauran soyayya da nufin gyara Allah ya ce zai daidaita tsakaninsu, amma idan shi ma ya gagara sai Allah ya ce Q2:226 “ Ga wadanda su ke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkiri na wata hudu, idan sun koma to lallai Allah mai gafara ne”

Wato idan namiji ya kauracewa gadon matarsa saboda sabani da ke tsakaninsu, kada ya wuce watanni hudu a wannan yanayi, domin wuce haka ya shiga hakkin ta. A wata na hudu ko dai ya koma kwanciya da ita ko ya sake ta. A gabar da saki ya halatta sai Allah cikin surar saki (Dalak) ya umarci manzon Allah da cewa Q65:2 “Ya kai Annabi idan kun saki mata sai ku sake su ga iddarsu”

Sharadin farko a saki shi ne ba za ka saki matarka ba sai ta na cikin tsarki, domin idan ka sake ta cikin jini sakin bai yiwu ba kamar yadda ya zo a hadisin Abu Dawood “Abdullah ibn Umar ya ruwaito cewa: AbdurRahman ibn Ayman ya tambayi Ibn Umar yayin da AbuzZubayr ke saurare: Me za ka ce game da mijin da ya saki matarsa a lokacin da ta ke jinin al’ada? Sai ya ce: Abdullah Dan Umar ya saki matarsa a lokacin da ta ke jinin haila a zamanin annabi (SAW) Sai Umar ya tambayi Annabi (Saw) cewa: Abdullah dan Umar ya saki matarsa ta na al’ada. Abdullahi ya ce: Ya dawo min da matata kuma bai saka sakin a matsayin saki ba. Ya ace: Idan ta yi tsarki, zai iya sakinta ko ya bar ta. Ibn Umar ya ce: sai Annabi (SAW) ya jawo ayar “Ya kai Annabi idan kun saki mata sai ku sake su ga iddarsu”. A nan tunda Annabi ya soke saki wanda aka yi shi lokacin da mace ke al’ada, ta yaya sannan za’a ce furuci ko ba niyya ya zama saki? A cikin wasan kwaikwayo?

Matsayi na gaba a cikin tsarin saki sai Allah ya ce Q2:229 “Saki sau biyu yake, sai a rika da alheri ko kuwa a sallama da kyautatawa”

Abin nufi shi ne saki sau daya ake yinsa bayan an biyo wadannan matakai, kuma za’a iya kome har sau biyu amma idan saki ya wuce biyu ya kai na uku to babu damar yin kome. To ko an yi saki daya sai Allah ya sake kafa wata ka’idar cewa Q65:6 “Ku zaunar da su daga inda kuka zauna daga gwargwadon samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku kuntata a kansu”

Wato bayan saki ba’a yarda mace ta kwashe kayanta ta yi gaba ba, sai ta zauna a dakin mijinta har sai ta gama iddarta. Hikimar wannan hukunci shine matukar tana zaune a gidan mijinta, zai wahala a kwashe watannin idda, matukar da ragowar soyayya tsakani a ce zuciyar waninsu ba ta karyo ba, kuma da zarar mijin ya kwanta da matar kafin ta gama iddar hakan ya mayar da auren tare da warware sakin. Wadannan matakai duk na zuwa ne a matsayin sakin farko, kuma haka za’a maimaita a saki na biyu. To da zarar an yi saki na biyu an kai wani siradi wanda Allah yace Q2:230 “Sannan idan ya sake ta (saki na uku) to ba ta halasta a gare shi daga baya, sai ta yi jima’i da wani miji, waninsa”

Wato kusa ta karshe da ake wa maza game da saki, shine idan ka kuskura ka yi saki na uku ba za ta sake dawo maka ba har sai ta yi wani auren kuma mijin ya take ta. Wannan tsoratarwa ce ga mazaje domin su guji saki sakaka.

A duk saki da za’a yi, na farko ne ko na biyu, babban sharadin da Allah ya tsayar (kuma shine wanda aka fi yin watsi da shi) shine fadar Allah cewa Q65:2 “Sannan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku rike su da abinda aka sani ko ku rabu da su da abinda aka sani kuma ku shaidar da masu adalci biyu daga gare ku”

Wannan shi ne matakin karshe na saki wanda sai an tabbatar da shaidu adilai guda biyu. Wadannan ne matakai da musulunci ya gindaya akan tsarin saki amma a yau sai aka wayi gari cewa sakin ake yi guda uku a lokaci guda kuma malamai har su na masa lakabin sakin bidi’a. Wannan sukurkucewa da aka bari na tsarin saki shi ya jefa al’ummar musulmi kasancewa ja-gaba wajen yawaitar mace-macen aure. Allah bai bada izinin yin saki a dunkule ba, kuma Annabi bai yi ba, amma daga baya an kallafawa musulmi yinsa sakamakon haka sai Allah ya ce mana a karshen wannan sura ta Dalak Q65:8-9 “Kuma da yawa daga alkarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umarnin ubangijinta da manzanninsa, sai muka yi mata hisabi, hisabi mai tsanani, kuma mu ka azabtar da ita, azabar kyama. Sannan ta dandana masifar al’amarinta. Kuma karshen al’amarinta ya kasance asara”

Hakika wannan al’umma tamu a yau na cikin wannan asara sakamakon watsi da wadancan ka’idoji da aka kafa mana game da sakin aure. Don haka muka fi kowa dandanar wannan masifa ta sake-saken aure a al’ummarmu. Mun wayi gari yau mun fi kowa yawan kananan zawarawa da ‘yaya a wargaje. A yau da ka bushi iska sai ka saki mace tamkar cire takalmi. Wani zai shekara arba’in tare da mace tun ba shi da ko sisi, ta tallafe shi wajen kulawa da bukatunsa na yau da kullum, ta kula da yayansa da duk wata mu’amalarsa, idan ya zama hamshakin mawadaci sai kawai rana daya, bayan ta gama shan duk wahalhalunsa kuma ya tsufar da ita, sai ya bushi iska ya ce na sake ki saki uku, kuma nan take ya ce ta kwashe kayanta. Akwai zalunci da ya kai haka? Kuma malamai sun daure gindin a yi haka? Ko su larabawa idan ka saki matarka sai dai ka fita ka bar mata gidan tare da dukiyar kula da ‘yayanta. Wannan ya sa saki da matular wahala a can. Haka su ma turawa saboda kudin alimony da zaka biya ya sa taka-tsantsan wajen saki. Ko a nan arewacin Najeriya abokan zamanmu kiristoci basa sakin aure irin mu. Mafi muni a al’amarin sakin aure na bahaushe, wanda ba saki ne irin na musulunci ba, ya sa ana danne hakkin yara da tagayyara su. A saki mace da yaya kuma a bar ta da dawainiyarsu ba tare da wani tallafi ba kuma gobe a auro wata. Ba zamu kaucewa wannan masifa ba har sai mun koma koyarwar Allah da manzonsa ta hakika na bin, sau-da-kafa, matakan da Allah ya gindaya mana a Qur’ani na yin saki, ko kuma mu ci gaba da dandanar masifar al’amarin da muka saka kan mu, na zama cikin azaba da asara wadda Allah ya gargade mu cikin waccan sura ta Dalak. Allah ya ganar da mu.

Ali Abubakar Sadiq ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Kano – Najeriya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan