Sheikh Bala Lau da Kabiru Gombe sun je yiwa Sanata Kwankwaso ta’aziyya

426

Shugabancin ƙungiyar ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iqamatus Sunnah, ƙarƙashin shugabanta Sheikh Bala Lau da Sakatarenta, Ustaz Kabiru Haruna Gombe, sun kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ziyarar ta’aziyyar rashin mahaifinsa.

Sheikh Bala Lau da Ustaz Kabiru Haruna Gombe sun kai ziyarar ta’aziyyar ne a gidan Sanata Kwankwaso da ke birnin tarayya Abuja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan