Majalisar masarautar Karaye da ke jihar Kano, bisa jagorancin Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar III ta amince da nadin Alhaji Saleh Musa Kwankwaso (Baba) a matsayin sabon Hakimin Madobi kuma Makaman Masarautar Karaye.
Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan harkokin kafafen yaɗa labarai na zamani, Salihu Tanko Yakasai, ya wallafa a shafinsa na facebook.

Nadin ya biyo bayan rasuwar mahaifin sa wato Marigayi Musa Saleh Kwankwaso Hakimin Madobi. Kafin naɗin sabon hakimin Madobin shi ne Dagacin Garin Kwankwaso
A ƙarshe sanarwar ta ce nan gaba kaɗan za a miƙawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje a rubuce wannan sabon nadin domin sahalewar sa.
Turawa Abokai