Kamfanin sadarwa da sada zumunta a yanar gizo na Facebook da ke ƙasar Amurka ya rufe shafin tashar Press TV mallakin ƙasar Iran, bisa dalilin cewa “Bai dace da dokokin amfani a shafukan sada zumunta ba”.
Sanarwar da Press TV ta fitar ta ce, “Facebook da ya yi ikirarin tashar Talabijin ta Iran ta Kasa da Kasa mai yada shirye-shirye a harshen Turanci ba ta dace da amfani da shafuka sada zumunta ba, ya rufe shafin tashar mai mabiya kusan miliyan 4.
A labaran an bayyana cewa, kamfanin Facebook ya sanar da tashar Press TV wannan mataki da ya dauka, saboda dalilai na tsaro ba wani dogon bayani da za a yi.
Turawa Abokai