Mai Bada Umarni A Kannywood, Ashiru Nagoma, Ya Samu Taɓin Hankali

156

Fitaccen mai bada umarni a finafinan Hausa na Kannywood, Ashiru Nagoma, ya samu larurar taɓin hankali.

Shafin Facebook na Kannywood da jaridar Intanet, Kadaura24 suka bayyana haka a ranar Alhamis.

A ranar Larabar da ta gabata, an wayi gari da ganin wasu hotuna na fitaccen mai bada umarnin na finafinan Hausa, hotunan da suka tabbatar da cewa ya samu taɓin hankali.

Bayyanar hotunan na Ashiru Nagoma ya janyo ka-ce-na-ce a kafafen sada zumunta, inda har aka fara zargin ‘yan Kannywood da ƙin taimaka masa don ya samu lafiya, kamar yadda Kadaura24 ta rawaito

Sai dai a wani martani da shahararren marubucin nan, Bala Anas Babinlata ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa Ashiru Nagoma ne kaɗai zai iya yi wa kansa magajin larurar da ya samu, ba ‘yan Kannywood ba.

“Ashiru Nagoma ne kaɗai zai iya yi wa kansa maganin haukansa ba ‘yan Kannywood ba. A rinƙa bincike don Allah”, in ji Anas.

Ashiru Nagoma ya yi fice a ɓangaren bada umarni a finafinan Kannywood, inda ya bada umarni a finafina kamar Nagari Na Kowa, Tutar so da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan