‘Yan Kwankwasiyya Fiye Da 2000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa Gandujiyya A Kano

320

Yayinda zaɓen ƙananan hukumomi ke ƙara ƙuratowa a jihar Kano, ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP tsagin Kwankwasiyya fiye da 2000 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙaramar hukumar Ungogo dake jihar.

Masu sauya sheƙar, waɗanda shugaban PDP na ƙaramar hukumar Ungogo, Magaji Gidan Jeji Rummawa ya jagoranta ranar Laraba, sun ce sun yanke hukuncin sauya sheƙar ne sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rashin cika alƙawura da suka riƙa fuskanta.

Magaji ya ce jam’iyyar ta sauka daga aƙidar Kwankwasiyya da aka ɗora ta a kai, kuma duk wani ƙoƙarin dawo da ita kan gwadabe da suka yi ya ci tura.

“Mun yi ta haƙuri da irin wahalar da muka riƙa sha, amma mun gano cewa muna ɓata lokaci ne idan muka ci gaba da zama a jam’iyyar. Haka kuma, mun yi imani kuma muna da ƙwarin gwiwa game da shugabancin Injiniya Abdullahi Garba Ramat a ƙaramar hukumar Ungogo”, in ji Magaji.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar, har da tsohon shugaban matasa na PDP a Ungogo, Ibrahim Sule Rangaza.

Da yake jawabi a yayin karɓar waɗanda suka sauya sheƙar, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, wanda shi ne ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar ta Ungogo, ya ce za a yi musu adalci.

Ya tabbatar musu da cewa za a yi wa dukkan ‘yan jam’iyyar adalci, kuma za a tafi da kowa.

Sai dai da yake tattaunawa da jaridar Intanet, Solacebase game da wannan al’amari, shugaban jam’iyyar PDP na Kano, Shehu Sagagi, ya ce ba shi da masaniya.

“A gaskiya ban san wani mambanmu da ya sauya sheƙa zuwa APC a yankin ba, saboda ba a sanar da ni haka ba”, in ji Shehu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan