Sha’aban Sharaɗa ya zargi Ganduje da hana ƴan ɓangaren Buhari takara

337

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano da Kewaye, Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada, ya zargi wasu makusantan Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da juyawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya, a lokacin fitar da ƴan takarar shugabancin ƙananan hukumomin jihar Kano.

Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana hakan ne, a yayin wata tattauna wa da aka yi dashi a wani gidan rediyo nai zaman kansa a Kano a jiya Alhamis.

Ɗan Majalisar ya ce babu wani ɗan ɓangaren shugaba Buhari da aka baiwa takarar shugaban ƙaramar hukuma ko ta Kansila a jihar Kano.

Haka kuma Honarabul Sha’aban ya ƙara da cewa waɗancan mutane da ya ke zargi, suna yiwa Ganduje ƙofar rago ne gabanin zaɓen shekarar 2023.

Har ila Yau Sha’aban Ibrahim Sharada ya musanta rahotonnin da ke cewar zai fita daga jam’iyyar APC.

A ƙarshe Sha’aban Ibrahim Sharada ya koka kan yadda wadancan mutane da yake zargi suka baiwa mataimakin gwamnan Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, kujerun Kansiloli 3 kowannen su, daga cikin kujerun Kansiloli 484.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan