A’lummar Kano Sun Ƙaurace Wa Zaɓen Ƙananan Hukumomi

154

Zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar ɗin nan a jihar Kano ya samu ƙarancin fitowar jama’a, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito.

Wakilin NAN da ya zagaya rumfunan zaɓe a cikin ƙwaryar birnin Kano ya rawaito cewa an samu ƙarancin fitowar jama’a a kusan dukkan rumfunan zaɓen.

Unguwannin da wakilin na NAN ya ziyarta sun haɗa da Ceɗi, Zage, Zango, Gandu, Sharaɗa, Wailawa, Ɗorayi, Kabuga, Rijiyar Zaki, Gwale da ƙaramar hukumar Ungogo.

A cewar NAN, an fara zaɓen ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe, inda aka jibge jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Sai dai wasu masu zaɓen da aka tattauna da su sun bayyana farin cikin bisa yadda suka kaɗa ƙuri’unsu.

Malam Jazuli Yusuf, wani mai zaɓe a Gwale ya ce ya yi zaɓen don ya sauke nauyi a matsayinsa na ɗan ƙasa.

Malam Jazuli ya ce wannan zaɓe zai ba masu zaɓe dama su zaɓi shugabanninsu a matakin ƙaramar hukuma.

Ita ma Malama Amina Isa, wata mai zaɓe a ungwar Zage, ta yaba wa masu zaɓen bisa yadda suka yi halin ɗa’a a yayin zaɓen.

Jam’iyyu 12 ne suka tsayar da ‘yan takara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 44 da kuma kujerun kansiloli 484, kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, KANSIEC ta bayyana.

KANSIEC ta kuma ɗauki ma’aikata 48,000 inda ta tura su rumfunan zaɓe 11,500.

‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro 10,000 ne suka bada tsaro a yayin gudanar da zaɓen.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan