Tabar Wiwi tana maganin ciwon Farfaɗiya – Bincike

653

Wasu likitoci da suka ƙware a wajen kula da masu fama da ciwon Farfaɗiya a ƙasar Australia sun gano cewa tabar Wiwi na warkar da masu fama da ciwon farfadiya.

Shugaban likitocin John Lawson ya bayyana haka inda ya kara da cewa sun gano haka ne a wani bincike da suka gudanar a jikin wasu yara dake fama da wannan ciwo su 40.

“Da muka gwada yin amfani da ganyen a jikin yaran sai kusan rabi daga cikin su suka warke, sauran da basu warke ba kuma suka sami saukin gaske daga ciwon.

Lawson ya ce duk da cewa binciken da suka gudanar ya samar musu da sakamako mai kyau, yayi kira da a cigaba da yin gwaji a akai domin samun nasara a kai mai nagarta.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kafa matakan da za su hana iyaye da mutanen da suke fama da wannan cutar yin amfani da tabar wiwi kai tsaye domin yin haka na tattare da matsala

Sannan ya yi kira ga gwamnatocin kasashe da su gaggauta sarrafa wannan magani domin hakan zai taimaka wajen hana mutane yin amfani da ganyen itacen kai tsaye.

Idan za a iya tunawa dai ƴan majalisar wakilai na Najeriya na yunkurin yin dokar da za ta halasta nomawa tare da kasuwancin Wiwi domin magani da yin kayan kwalliya da bincike da kuma samar da kudaden shiga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan