Tunawa Da Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato— Daga Aliyu Ibrahim Sani Mainagge

192

A ranar 15 ga Janairu, 1966, aka wayi gari da labarin kisan gilla tare da juyin mulki da su; Manjo Patrick Chukwumeka Kaduna Nzeogwu, Donatus Okafor, E. A. Efeajuna da sauransu suka shirya wanda ya hamɓarar da halattacciyar gwamnatin farar hula, kuma ya yi sanadiyyar kashe Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Birgediya Janar Zakariyya Mai Malari, Kur Muhammad, Laftanar Kanar J. Y. Pam, Kanar Shodeinde da sauransu.

Wannan juyin mulki da kashe waɗannan yan mazan jiya, shi ne ya canza alƙiblar Najeriya da tsarin zamantakewa da siyasarta.

An haifi Alhaji Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, kuma Firimiyan Yankin Arewa na Najeriya, a shekarar 1909. Ahmadu Bello jika ne ga Mujaddadi, Shehu Usman Ɗan Fodiyo.

Sardauna shi ne mafi tasiri a siyasar Arewacin Nijeria, kai bayan kakansa Mujaddadi Shehu Usman Ɗan Fodiyo (Allah Ya yi masa rahama) ba a yi mutumin dake da tasiri a siyasa da zamantakewar alumma kamar Sardauna ba. Ya yi alaƙa ta kusa da manyan shugabannin duniya, musamman ƙasashen Larabawa da suka haɗa da; Sarki Faisal Ɗan Abdul’aziz da Shugaban Misra, Jamal Abdun-Nasir, sannan ya yi abota ta kusa da manyan malamai da masu kishin addini da suka haɗar da; Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Ibrahim Inyas da Sayyid Quɗub Ibrahim na Misra.

Mutum ne mai kishin Musulunci, wanda da taimakon Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi suka kafa Ƙungiyar Jamaatu Nasril Islam, JNI, wadda ta zama ƙungiyar Musulmi mafi girma a Najeriya ta Arewa, kuma ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Musulmi ta Duniya, watau Rabiɗatul Alamil Islamiy ko World Muslim League.

Bayan kishin addini, Ahmadu Bello mutum ne mai tsananin kishi da yin aiki tuƙuru don taimaka wa alummarsa, yakan ce, Idan ina tafiya, ina ganin yadda jamaar dake zaune a ƙauyuka suke ta noma da irin faretanin da iyayensu da kakanninsu suka yi amfani da su tun da, sun duƙufa ga aikin dake gabansu ga matsanancin zafin rana na ta dukan bayansu, matansu da yayansu su zo suna taimakon su, na kan yi ta ganin mutane waɗanda cuta ke neman kashewa saboda sun cika zama nesa daga wurin da asibiti yake balle su je su sami taimako. Da rani kuma, na kan ga irin ƙarancin ruwan sha da ake fama da shi To me zamu yi da zai jawo sauƙin waɗannan alamura?. (Duba littafin Rayuwata na Ahmadu Bello, Bugawar Cambridge University, 1962).

A ƙarshen rayuwarsa, sojojin Inyamurai Kiristoci, sun zarge shi da ƙoƙarin Musuluntar da Najeriya da kuma ƙaddamar da jihadi, kamar yadda Manjo Patrick Chukwumeka Kaduna Nzeogwu ya shaida wa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wanda wannan ne ta sanya suka shirya juyin mulki da kuma aiwatar da mummunan kisan gilla gare shi da sauran mutanen da muka ambata a sama.

Muna roqon Allah ya karɓi Sir. Ahmadu Bello da Alh. (Sir.) Abubakar Tafawa Ɓalewa a matsayin shahidai. Allah Ya gyara shuwagannin Musulmi, Ya sanya musu kishin alummarsu da addininsu.

Aliyu Ibrabim Sani Mainagge malami ne, marubuci kuma manazarci.
Ya rubuto daga Kano.
Za a iya samun sa a kan lambar waya: 08068985599, ko adireshin imel: alibabapress2021@gmail.com.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan