A ƙalla mutane 23 ne suka mutu a Norway bayan sun karɓi riga-kafin COVID-19 ta kamfanin Pfizer, mutum 13 daga cikin su waɗanda suke karɓar magani ne daga gida, a cewar jami’an lafiya.
Abubuwan da aka gani bayan riga-kafin da suka haɗa da zazzaɓi da tashin zuciya “ka iya zama abubuwan da suka bada gudunmawa wajen samun mummunan sakamako a tsakanin wasu marasa lafiya”, in ji Sigurd Hortemo, Babban Likita a Hukumar Haɗa Magunguna ta Norway a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Dukkan mutanen 13 marasa lafiya ne masu karɓar magani a gida, kuma sun kai a ƙalla shekara 80.
Jami’an lafiya ba su nuna damuwa ba game da wannan al’amari, maimakon haka suna ƙara shiri don gano waɗanda ya kamata su karɓi riga-kafin.
Wannan labari ya zo ne mako ɗaya bayan jami’an lafiya sun bada rahoton mutuwar wasu marasa lafiya biyu masu karɓar magani a gida bayan sun karɓi riga-kafin COVID-19 ɗin na kamfanin Pfizer.
Fiye da mutum 30,000 a Norway sun karɓi kason farko na riga-kafin, a cewar alƙaluman da jami’an lafiya suka fitar.
“Ba mu san haka za ta faru ba”, Steinar Madsen, Shugaban Hukumar Haɗa Magunguna ta Norway ya faɗa wa wa gidan rediyon NRK na Norway haka.
“A fili yake cewa waɗannan riga-kafin ba su da haɗari sosai, sai dai ga marasa lafiya da suka fi shiga fi shiga wahala.
“Yanzu dole likitoci su kula sosai game da wa ya kamata a yi wa riga-kafi”, ya ƙara da haka.
“Waɗanda suke jin jiki sosai kuma suka tsufa sosai za a iya yi musu riga-kafin bayan an duba su a ɗaiɗaikun su”, in ji shi.
Wani wakilin kamfanin Pfizer ya ce kamfanin “yana sane da rahotannin mace-macen bayan yin riga-kafin a Norway kuma yana nan yana aiki da Hukumar Haɗa Magunguna ta Norway don tattara dukkan bayanan da suka kamata”.