Sanata Barau Jibrin ya ƙauracewa zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Kano

234

Sanata mai wakiltar mazaɓar Arewacin Kano a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Ibrahim Jibrin, da wasu daga cikin ƴan majalisar wakilai sun ƙauracewa zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kano.

Haka kuma ba a iya fuskar Sanata Barau Jibrin kaɗice aka ƙi gani ba, har da sauran ƴan majalisar wakilai kamar su Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa, sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharaɗa da ke waklitar ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye.

A jiya ne dai aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi arba’in da huɗu a jihar Kano, inda jam’iyyar APC ta lashe zaɓen.

Tuni dai al’ummar jihar Kano su ka fara tofa albarkacin bakinsu a game da rashin ganin Sanatan wanda ya daɗe da bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Kano a kakar zaɓen shekarar 2023.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan