Sarki Muhammad Sanusi II ya kaiwa Sanata Kwankwaso ta’aziyyar rashin mahaifinsa

380

Wakilin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, Alhaji Mannir Sanusi (Danburan din Kano) ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Mannir Sanusi Da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Tun da farko mataimaki na musamman akan kafafen yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ne ya wallafa hotunan ziyarar ta’aziyyar a shafin Sanata Rabi’u Kwankwaso na facebook.

Manniru Sanusi Da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

A cikin watan Disambar shekarar bara ne Allah ya yi wa Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano rasuwa

Turawa Abokai

2 Sako

  1. Alhamdulillah muna godiya ga Allah subhanahu wata’allah dayanuna muna wannan rana da tsohon sarki sanusi na II yakawowa senato kwankwaso ta’azeya rashin mahaifinsa mun godiya mu’yan kwankwasiyya aman

  2. Idan ma Musa ilyasu yace shi ya koyawa Rabiu Musa kwankwaso siyasa me yasa a yanxu ake kallon Kwankwaso a matsayin mai gidan mai gidan watau Abdullahi Umar Ganduje?
    Zaban kananan hukumomi ai da man an San Wanda zaici Zaben, jam’iyya mai mulki kawai shi yasa ma ban fito, na zauna a Gida nata ya momy na aiki na sanitation.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan