Yadda ƴan soshiyal midiya su ka zama shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

414

Fitattun ƴan Soshiyal Midiyar nan na jam’iyyar APC a jihar Kano, wato Faizu Alfindiki da kuma Auwalu Lawan Aranposu na daga cikin jerin sababbin shugabannin ƙananan hukumomi arba’in da huɗu da aka zaɓa a jihar Kano.

Faizu Alfindiki wanda ya yi suna wajen adawa da manufofin siysar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma sukar tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ya lashe zaɓen shugabancin ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye.

Honarabul Faizu Alfindiki

Haka kuma kafin zaɓen Faizu Alfindiki a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, shi ne mai taimakawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan harkokin gwamnati.

Shi kuma Auwalu Lawan Aranposu ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, duk da cewa ya fuskanci zazzafar adawa daga cikin gidan jam’iyyar APC reshen ƙaramar hukumar ta Nasarawa.

Honarabul Auwalu Lawan Aranposu

Hakazalika kafin zaɓen na sa shi ne mataimaki na musamman ga gwamna Ganduje akan harkokin fasahar sadarwa zamani.

Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na kallon hakan a matsayin wani cigaba a harkokin siyasa, la’akari da irin rawar da ƴan Soshiyal Midiyar ke takawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan