Home / Labarai / Ƴan Najeriya miliyan 15 ne ke ta’amali da miyagun ƙwayoyi – Buba Marwa

Ƴan Najeriya miliyan 15 ne ke ta’amali da miyagun ƙwayoyi – Buba Marwa

Tsohon gwamann soja a jihar Legas Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, kuma sabon shugaban Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa wato NDLEA, ya bayyana cewa kimanin ƴan Najeriya miliyan goma sha biyar ne su ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Janar Buba Marwa ya ce daga yanzu, ya sa ƙafar wando guda da masu wannan mummunar ɗabi’ar tare kuma da yaƙi da masu safararta gadan – gadan.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi dai gagrumar matsala ce da ta addabi Najeriya.

Ko a cikin shekarar 2018 sai da gida rediyon BBC ya fitar da wani rahoto kan binciken da ya yi a kan matsalar shaye-shaye, inda ta gano hannun wasu kamfanonin sarrafa magunguna.

Hakan ne kuma ya kai ga gwamnatin kasar rufe kamfanonin tare da haramta amfani da sinadarin kodine da ke kara jefa rayuwar matasan kasar cikin haɗari.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Yadda aka yi addu’ar cikar Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa shekara 1 a kan mulki

Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *